A ganawar da ta gudana tsakanin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Lavrof da shugabar kungiyar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini-Zuma a cibiyar kungiyar ta tarayyar Afrika da ke birnin Addis Ababa na kasar Habasha; bangarorin biyu sun jaddada muhimmancin karfafa alaka a tsakaninsu tare da gudanar da taimakekkeniya a bangarori da dama da nufin habaka ci gaban kasashensu, sannan suka rattaba hannu kan takardar yarjejeniya kan muhimman batutuwan da suka cimma a yayin zaman tattaunawan da ya gudana a tsakaninsu.
Shugabar kungiyar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini Zuma ta jaddada muhimmancin karfafa alaka da taimakekkeniya tsakanin kungiyarta da kasar Rasha a fuskokin da suka shafi harkar ilimi, fasahar kere-kere, harkar noma, fasahar kimiyya da kuma uwa uba kokarin wanzar da zaman lafiya da sulhu a kasashen nahiyar Afrika. ABNA