Zuwa yanzu dai babu wani bature da ya kamu da cutar amma cutar ta shafi wasu Amurkawa guda biyu.
Kungiyar Likitocin Doctors Without Borders ta yi gargadin cewa cutar Ebola yanzu ta zama annoba, domin zata iya yaduwa zuwa kasashe da dama. Domin yaki da cutar ne kuma kungiyar Tarayyar turai ta amince da wasu karin kudin tallafi sama da euro Miliyan biyu tare da tura kwararru zuwa inda cutar ta yi kamari.
Jiragen sama da dama ne suka dakatar da jigila zuwa Liberia da Saliyo saboda fargabar yaduwar cutar zuwa wasu kasashe, musamman wani mutumin Liberia da ya kai cutar a Najeriya kafin ya mutu a lagos.
Ma’aikatar harakokin wajen Birtaniya tace cutar ebola barazana ce ga Ingila, yayin da tuni bangaren kula da lafiyar al’umma a Birtaniya ya yi gargadi zuwa ga likitocin kasar su dauki matakai.
Cutar Ebola dai ta kashe mutane 672, cikin su har da likitan Saliyo da ke kula da wanda da suka kamu da cutar eboala. ABNA