30 Yuli 2014 - 07:58
Likitan da ke kula da Ebola ya mutu a Saliyo

Babban likitan da ke kula da da fannin kawar da cutar Ebola a kasar Saliyo ya mutu, bayan kamuwa da cutar. Dr Sheikh Umar Khan ya yi suna wajen warkar da mutane kusan 100 da suka kamu da wannan cuta da ke kisan Jama’a a yammacin Afrika.

Umar Khan ya rasu ne a wata babbar asibitin Saliyo da misalin karfe biyu na rana a jiya Talata.

Kafin kamuwa da cutar, Likitan shi ke jagorantar aikin warkar da cutar Ebola a wata asibitin garin Kenama da ke gabas da birnin Freetown.

Alkalumman lafiya a kasar Saliyo sun ce kimanin mutane 489 suka kamu da cutar Ebola a kasar Saliyo, yayin da 159 suka mutu. ABNA