25 Yuli 2014 - 14:05
Ana Gudanar Da Jerin Gwanon Ranar Quds Ta Duniya A Iran Da Sauran Kasashe

A yau ne ake gudanar da jerin gwano gami da tarukan na ranar Quds ta duniya a kasa daban-daban, domin da kisan Kiyashi da Isra'ila take yi wa Palastinawa a Gaza da sauran yankunan Palastinu, tare da keta alfarmar wurare masu masu tsarki.

Tun da safiyar ne miliyoyin mutane suka fara gudanar da wannan jerin gwano a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar muslunci ta Iran da kuma sauran biranan kasar Iran baki daya, inda ake rera taken mutuwa ga Isra'ila 'yanci ga al'ummar Palastinu, kamar yadda wasu suka daga hotunan kananan yara da Haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi wa kisan gilla a zirin Gaza.

Ana gudanar da irin wannan jerin gwano a birane daban-daban na kasashen duniya, da suka hada har da biranan wasu kasashen turai da Latin Amurka, da nahiyar Afirka da kuma wasu kasashen Asia, domin nuna goyon baya ga al'ummar palastinu, da kuma yin Allawadai da zaluncin da suke fama da shi daga yahudawan sahyuniya tsawon shekaru fiye da 60