A hudubar sallar juma’arsa ta yau a birnin Karbala na kasar Iraki Sheikh Abdul-Mahdi Al-Karbala’i wakilin babban malamin addinin Musulunci a Iraki Ayatullahi Sistani ya bayyana cewa; Ayatullahi Aliyu Sistani ya bukaci dukkanin al’ummar Iraki da su daura damara tare da sabar makamai domin yakar ‘yan ta’adda da nufin kare kasar Iraki.
Sheikh Karbala’i ya kara da cewa; Babban hatsari yana barazana ga kasar Iraki don haka wajibi ne a kan mutanen da suke da damar daukar makami su shiga cikin sahun jami’an tsaron Iraki domin kare kasar, kuma duk wanda ya mutum ya yi shahada a matsayin shahidi.
A nashi bangaren Sayyid Muktadha Sadar ya kira yi magoya bayansa da dukkanin al’ummar Iraki da su shiga cikin sahun jami’an tsaron Iraki wajen kare kasar daga babban hatsarin da take fuskanta.ABNA