An dai yi musayar fursunonin 5 ne da wani Sojan Amurka Sergeant Bow Bergddhl, wanda shi ne soja guda da ya rage a hannun 'yan Taliban fiye da shekaru 4 a Afghanistan.
A wani jawabi da ya yi wa manema labarai a fadar White House, Mr. Obama ya gode wa gwamnatin kasar Qatar din kan shiga tsakanin da ta yi wajen tattaunawa tsakanin Amurka da kungiyar Taliban.
''Mun himmatu wajen ganin mun kawo karshen yakin da ake a Afghanistan kuma mun himmatu wajen ganin mun rufe sansanin Guantanamo. Mun lashi takobin ganin mun dawo da fursunoninmu na yaki gida'' inji shi.ABNA