21 Mayu 2014 - 10:14

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya ta ce adadin wadanda suka mutu daga tagwayen hare-haren bom din da aka kai jiya a Jos babban birnin jihar Filato ya kai 118.

Haka ma hukumar ta ce wadanda kuma suka samu raunuka a harin na ranar Talata sun kai 84.

Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa harin farko na kunar bakin wake ne, amma mota ta biyu da ke dauke da bam ta fashe ne mintoci kadan bayan fashewar ta farkon.

Har izuwa yanzu dai babu wata Kungiya da ta dauki alhakin harin.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi tur da harin da aka kai Jos, babban birnin Jihar Filato, yana bayyana maharan da cewa makiya 'yancin bil Adama ne.ABNA.