18 Mayu 2014 - 16:10
An Kawo Karshen Aikin Ceto A Turkiyya.

An Kawo Karshen Aikin Ceto A Mahakar SOMA Data Ruguje A Turkiyya.

Masu aikin ceto sun kawo karshen ayyukan binciken da suke a ma'aikatar hako da Mu'adanai SOMA a kasar Turkiya, bayan da suka samo gawa ta karshe da ta kai ga adadin mutun 301 na wadanda suka mutu sakamakon rugujewar wannan ma'aikata ta kalkashin kasa.   Yau dai kwanaki biyar da afkuwar lamarin wanda ya tayar da zanga-zanga kusan a ko'ina cikin fadin kasar ta Turkiya, inda masu zanga-zangar ke neman Firaminista Recep Tayyip Erdogan, da ya yi murabus sabili da acewar su sakacin hukuma ce, ya kai ga mutuwar daruruwan mutanen wannan ma'aikata.   Ran Juma'a dai sai da jamiyan tsaro na 'yan sanda suka tarwatsa wata zanga-zangar ta mutane fiye da dubu 10 a Soma inda hadarin ya faru, inda yan sandar sukayi amfani da hayaki mai sa kwalla da kuma fesa ruwa mai karfin gaske wajan tarwatsa masu zanga-zangar.ABNA.