Yayin da yake sanar da adadin mutanen ministan makamashin Turkiyya Taniya Yeldez yace adadin mutanen da suka mutu din yayin wannan hatsarin ya karu zuwa mutane 201 sannan wasu daruruwa kuma suna nan makale a cikin kasa din yana mai cewa lokaci na ci gaba da kurewa dangane da batun ceto su.
Wannan lamarin dai ya faru ne bayan fashewar wani abu kimanin kilomita biyu a karkashin kasa lamarin da ya janyo katsewar wutar lantarki tare da toshewar hanyar shakar iska.
Rahotannin sun ce da dama daga cikin wadanda suka rasa rayukan na su sun mutu ne sakamakon shakar gubar sinadirin Carbon Monoxide bayan fashewar.ABNA.