Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Ma'aikatar a cikin wata sanarwa da ta fitar, a yau Laraba, ta nanata haƙƙin Lebanon na asali na kare amincin yankunta da ikonta na ƙasa, tana mai nanata goyon bayan Tehran ga Lebanon wajen kare 'yancin kanta da ikonta na ƙasa da haɗin kan yankunta.
A wani yanayi mai alaƙa, ma'aikatar harkokin waje ta Iran ta yi Allah-wadai da "tsoma baki da katsalandan din Amurka mai mummanar niyya" cikin al'amuran cikin gida na Lebanon.
Ma'aikatar ta ɗauki motsin Washington na ƙirƙirar hanyoyin da ba su da amincewar al’ummar ƙasar a matsayin haɗari mai tsanani ga 'yancin kai na Lebanon da amincinta da haɗin kan ƙasarta.
Ta kuma yi nuni da cewa waɗannan shiga shar oba shanu na Amurka na nufin buɗe wata hanya wajen ƙarfafa "mugunyar manufofin siyasarta" da mamayar gwamnatin Isra'ila.
Wannan yana zuwa ne a lokacin da hare-hare da mamayewar Isra'ila ke ci gaba a yankuna da dama na kudancin Lebanon, a tsakiyar motsin fagen daga da ke tafiya tare da harba manyan bindigogi da fashe-fashe da hare-hare ta sama, ban da tashin jirage marasa matuƙa na Isra'ila kowace rana a sararin samaniyar Beirut da kewayenta, a bayyanannen keta ikon ƙasar Lebanon da "yarjejeniyar dakatar da bude wuta."
…………
Ra'ayinka