Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Hedkwatar Khatam al-Anbiya, tare da fitar da wata sanarwa, ta yi gargadin cewa, duk wani kamfani ko ƙasa da ta karɓi wani kuɗi daga dukiyoyin Iran, ba za ta sami izinin wucewa ta mashigar Hormuz ba.
Sanarwar tazo kamar haka yake:
Bismillahir Rahmanir Rahim
Shugaban Amurka, a cikin ayyukansa na ta'addanci, da kuma ƙoƙarinsa na ci gaba da dagula yankin, ya sanar da cewa, zai biya diyyar jiragen ruwan da aka lalata a yayin yaƙin da yake akan Iran Musulunci daga cikin dukiyoyin da aka daskare na Iran, wanda hakan ya faru saboda rashin tsaro da sojojin Amurka suka haifar, da kuma keta doka ta hanyar wucewa ta hanyar da ba ta dace ba kuma marar tsaro a kudancin mashigar Hurmuz,.
Yayin da muke yin gargadi ga shugaban Amurka dan ta’adda game da sakamakon wannan matakin da ba bisa ka'ida ba, muna sanar da dukkan kamfanoni da ƙasashen da za su karɓi shawarar Trump, kuma su yi amfani da dukiyoyin da aka daskare na Iran a ƙarƙashin wannan taken, cewa, daga yanzu, sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ba za su ba da izinin wucewa ta mashigar Hurmuz ga kowane jirgin ruwan su ba.
Kuma babu wani taimako da nasara face daga wurin Allah Mabuwayi Mai Hikima.
.............
Ra'ayinka