17 Yuni 2026 - 09:34
Source: ABNA24
Girmamawa, Fahimta Da Goyon Baya; Ginshiƙai Uku Na Zamantakewar Aure Mai Dorewa

A cikin litattafan tarbiyya da yawa an ce mace da namiji suna fitowa daga iyalai biyu, al'adu biyu da kuma gogewa biyu daban-daban. Don haka a dabi’ance ra'ayinsu game da rayuwa, shaukinsu da ma matsaloli su bambanta. Amma idan aka sarrafa waɗannan bambance-bambancen yadda ya kamata, suna haifar da habakar kaunar juna maimakon nisantar juna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: A cikin duniyar da dangantaka da zamantakewar aure ke ƙara rikicewa da tabarbarewa kowace rana, amma wata gaskiya mai sauƙi har yanzu tana haskakawa kamar ranar farko: Babu wata dangantaka da za ta dawwama ba tare da girmamawa, fahimtar juna da martani mai kyau ba.

Rayuwar aure ba wai kawai zama tare ba ce; fasaha ce ta gani, ji da fahimtar juna.

A ci gaba, za mu yi nazari kan manyan ginshiƙai guda uku na dangantaka mai lafiya da inganci tsakanin ma’aurata daga cikin maganganun masana da koyarwar ɗabi'a; ginshiƙan da idan aka ƙarfafa su a rayuwar aure, gida zai zama wuri mafi aminci a duniya.

1. Girmamawar Juna; Harshen Soyayya Na Farko

Girmamawa ba wai kawai ɗabi'a ba ce; sarari ne da mutane za su iya zama ainihin kansu tare da nuna asalinsu da yadda zatinsu ya kasance.

Lokacin da mace da namiji suka saurari maganar juna, suka yarda da bambance-bambancen juna, kuma suka tsaya tare a lokacin damuwa, zasu zamo masu mayar da girmamawa daga fada da baki zuwa a aikace.

Girmamawa na nufin:

- Idan matarka ko mijinki ya ke cikin damuwa, kada ka/ki katse maganarsa ma’ana ki/ka bar shi ya karasa fadar abinda ya ke damunsa

- Kada ki/ka ɗauki bambance-bambancensa a matsayin rauni

- Kada ka raina shi/ta a cikin jama'a

- Kuma a keɓe, ka kira shi/ta da kyakkyawan lafazi cikin tausasawa.

A cikin wasu litattafan halayya an ce yadda kake kiran abokin zamantakewar aurenka zai iya shafar jin girmamawa.

Wannan yana nufin cewa ƙananan halaye suna isar da manyan saƙonni.

2. Fahimtar Juna; Gadar Tsallake Nisanta Ga Kai Zuwa Ga Zurfafawar Kauna

Babu wata dangantaka da ke ci gaba da zato da hasashe.

Dole ne mace da namiji su tsallake "nisa na zahiri" don su kai ga "zurfin tunani ga junansu".

Fahimta na nufin:

- Mu ɗauki jin daɗin juna da muhimmanci

- Mu rika yiwa juna suka wacce ta da ce “ma’ana idan daya yayi abinda bai dace  ba kayi masa Magana ya gyara alokacin da ya dace da kalaman da suka da ce”.

- Ka Da Mu rika jin tsoron faɗar buƙatunmu ga juna

- Kuma mu bar abokinmu zamantakewar aurenmu ya san mu yadda muke

Fahimta ta gaske tana faruwa ne lokacin da mace da namiji suka yi magana game da abinda suke ji ajikinsu da ruhinsu da buƙatu da rauninsu a tsakaninsu ba tare da tsoron mai da martanin juna ba.

Suka ko korafi cikin ladabi da girmamawa, ba alama ce ta rashin girmamawa ba; alama ce cewa dangantaka tana da muhimmanci a gare mu.

3. Martani Mai Dacewa Da Hankali; Fasahar Fahimtar Lokaci

Wani lokaci matsalar dangantaka ba "rashin soyayya da kaunaa" ba ce; a’a Rashin martani mai kyau a lokacin da ya dace ne.

Dole ne mace da namiji su koyi:

- Lokacin da za su yi shiru

- Lokacin da za su yi magana

- Lokacin da za su taimaka

- Kuma lokacin da za su saurara kawai ga dayansu

Hankali mai dacewa yana nufin mu fahimci abokin aurenmu me ya ke buƙatar a yanzu:

Ƙarfafawa?

Kaɗaici?

Tattaunawa?

Ko dubi gareshi cikin nutsuwa kawai?

Wannan ƙwarewa tana ceton dangantaka daga rashin fahimta kuma tana ba ta zurfi.

4. Bambance-Bambance Ba Abin Ki Ba Ne; Su Ne Kayayyakin Gina Zamantakewar Aure

A cikin litattafan tarbiyya da yawa an ce mace da namiji suna fitowa daga iyalai biyu, al'adu biyu da kuma gogewa biyu daban-daban.

Don haka a dabi’ance ra'ayinsu game da rayuwa, ji da ma matsaloli sun bambanta.

Amma idan aka sarrafa waɗannan bambance-bambancen yadda ya kamata, suna haifar da girma da habakar alakar juna maimakon nisantar juna.

Dole ne mace da namiji su koyi:

- Maimakon su canza juna, su fahimci juna

- Maimakon su kwatantanta juna, su yi haɗin kai

- Kuma maimakon su yi hukunci akan abu kai tsaye, su tattauna da juna

5. Dangantaka Mai Dorewa, Danganta Ce Da Ake Gina Ta

Babu wata dangantaka mai lafiya mai inganci da ke faruwa "kwatsam" sai dai ana gina ta ne.

Girmamawa, fahimta da martani mai kyau, ƙwarewa ce guda uku da dole ne a yi hori juna a kansu kowace rana.

Lokacin da mace da namiji suka:

- Yi magana da girmamawa

- Suka fahimci juna

- Kuma suka mayar da martani da hankali

Gida zai zama wurin da kwanciyar hankali ke gudana, soyayya ke numfashi, kuma rayuwa ta sami ma'ana.

Marubuciya: Malama Fatima Pour Abbas

Fassara: Editan ABNA Sashen Hausa

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha