14 Yuni 2026 - 09:12
Source: ABNA24
CAIR: Ta Yi Allah-wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Gidan Malami Musulmi A Burtaniya

An kai wa gidan wani malami hari da kone-kone a Bolton a Ingila — wanda wata babbar ƙungiyar kare hakkin Musulmi a Amurka ta bayyana ra'ayinta game da lamarin in da tai Allah wadai da wannan mummunan harin.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Majalisar Harkokin Musulunci da Amurka (CAIR), babbar ƙungiyar kare hakkin jama'a da kare Musulmi a ƙasar, a ranar Alhamis ta bayyana goyon bayanta ga al'ummar Musulmi na Birtaniya bayan harin da aka kai wa gidan wani limamin da iyalinsa a Bolton da kone-kone. CAIR ta kuma yi Allah-wadai da tarzomar wariyar launin fata da ta faru a Arewacin Ireland.

An fitar da hotunan kyamarori na tsaro da ke nuna wani mutum da ya rufe fuska yana kai harin da ake zargi na kone-kone a gidan limamin. 'Yan sanda sun tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike, kuma har yanzu ba a kama kowa ba.

A cikin kwanaki biyu da suka gabata, an yi tarzomar wariyar launin fata a Arewacin Ireland. 'Yan sanda sun yi amfani da bindigogin ruwa da harsashin roba don tarwatsa masu zanga-zangar.

A cikin wata sanarwa, CAIR mai hedikwata a Washington, D.C., ta ce:

"Muna bayyana goyon bayanmu ga limamin da iyalinsa a Bolton, da kuma al'ummar Musulmi a duk faɗin Burtaniya. Mun yi Allah-wadai da tashin hankalin kin Musulmi da kin bakin haure da ke addabar Turai, kuma muna kira ga dukkan shugabanni da su yi allah wadai da hakan. Kalaman kin Musulmi da kyamar baki da suka mamaye al'ummomin Turai suke haifar da irin tashin hankalin da muke gani."

CAIR ta kuma jaddada cewa magajin garin babban birnin Paris ya nuna bacin ransa a ranar Alhamis bayan bayyanar wata tuta a babban cocin gida da ke kiran korar jama'a.

………………………………

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha