15 Yuni 2026 - 12:12
Source: ABNA24
Nasarar Iran Daga Kallafaffen Yaƙi Zuwa Yarjejeniya; Nasarar Al'umma A Kan Babban Shirin Mika Wuyai Da Rushewa

Yau, ita ce ranar da Iran ta ci gaba da wanzuwa; ba wai kawai ta ci gaba da wanzuwa ba, har ma ta soke hasashe da tsare-tsare da yawa da aka rubuta game da makomarta. Wannan shine batun da tarihi zai rubuta game da ita...

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) na Duniya - ABNA: A cikin tarihin al'ummomi, akwai wasu lokuttan da suka wuce nasarar soji ko nasarar siyasa, lokuttan da suka zama juyi mai mahimmanci wajen tabbatar da "asalin ƙasa". Abin da Iran ta sha fama da shi a cikin 'yan watannin da suka gabata yana daga cikin irin wannan lamari; yaƙin da manufarsa ba wai kawai jawo asarar soji ko matsin siyasa ba ne, a'a, ƙoƙari ne na tsari da shiri don sauya hanyar al'umma da karya ƙudurin ƙasa.

Tun daga farkon kwanakin da aka fara aikin karya ƙuduri da yunkurin kai al'ummar Iran ga mika wuya, manufofin Amurka, gwamnatin yahudawa da kawayensu na bayyane da na boye sun kasance a sarari. Suna magana game da mika wuya ba tare da wani sharadi ba, suna magana game da canza tsarin mulki, suna magana game da karya fagen gwagwarmaya, kuma suna fatan cewa matsin lamba a lokaci guda na soji, tattalin arziki, kafofin yada labarai da na tunani zai iya tilasta Iran ta ja da baya. Amma a yau, bayan fiye da dare da rana ɗari na juriya, babbar tambaya ita ce, wanne daga cikin waɗancan manufofin ya cimma?

Tsare-tsare da shirye-shiryen makiya da suka ruguje daya bayan daya:

- Ana tsammanin Iran za ta fuskanci hargitsi a cikin gida; hakan bai faru ba.

- Ana tsammanin rarrabuwar kawuna tsakanin jama'a da gwamnati za su yi zurfi; hakan bai faru ba.

- Ana tsammanin sojoji za su rasa haɗin kai; hakan bai faru ba.

- Ana tsammanin muhimman ababen more rayuwa na ƙasar za su daina aiki; hakan bai faru ba.

- Ana tsammanin shugabannin siyasa da diflomasiyya na ƙasar za su ja da baya daga nauyin da ya hau kansu; hakan bai faru ba.

- Ana tsammanin 'yan adawa da ke zaune a waje za a gabatar da su a matsayin madadin hukumar Iran; hakan bai faru ba.

- Ana tsammanin canjin tsarin mulki zai faru a matsayin sakamakon yaƙin; hakan bai faru ba.

A zahiri, abin da ya ruguje ba tsarin Iran ba ne, a'a, tarin lissafai da ƙididdiga ne da aka gina a cikin shekaru da yawa a cikin dakunan tunani na yamma game da Iran.

Babban Asirin; Rashin Nasarar Yaƙi Kan Ƙudurin Azamar Al’ummar Iran

Sabanin abin da ake zato, muhimmin fagen wannan yaƙi ba fagen soji ba ne; a'a ba haka abin ya ke ba sai dai, babban yaƙin ya gudana ne a fagen ƙudurar azama.

Masu tsara matsin lamba mafi girma sun yi tunanin cewa al'ummar Iran ba za ta iya jure wa yaƙi mai tsawo ba, kuma tare da ƙara matsin lamba, haɗin kan ƙasa zai ɓace bat. Amma ƙwarewar 'yan watannin da suka gabata ta nuna cewa a lokuta masu mahimmanci, al'ummar Iran har yanzu tana da ƙarfin tarihi don kare 'yancin kanta da yankin ƙasarta.

Wannan ita ce gaskiyar da yawancin manazarta na waje suka kasa sanyawa a cikin lissafinsu; cewa Iran ba wai kawai tsarin siyasa ba ce, a'a, asali ne na tarihi da wayewa, kuma barazana ga wanzuwarta, maimakon haifar da rugujewa, yana haifar da haɗin kai mai zurfi ne.

Iran; Daga Batun Tabarbarewa Zuwa Yar Wasa Mai Tasiri Mai Mahimmanci

Wani muhimmin sakamako na wannan arangama, canjin matsayin Iran a cikin ma'auni na yanki da na duniya ne. Ƙasar da ake tsammanin za’a tilasta mata yarda da sharuɗɗan wasu a ƙarƙashin matsin lamba, a ƙarshe ta sa bangaren da ke gaba ya sake duba lissafinsa. Wannan ci gaban ya nuna cewa zamanin yanke hukunci ga al'ummomi yana zuwa ƙarshe, kuma manyan ƙasashe ma dole ne su yarda da gaskiyar fagen fama.

A cikin wannan, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sami damar nuna cewa ko a cikin mawuyacin yanayi, tana da ikon kiyaye kwanciyar hankali na cikin gida, gudanarwa da iya sarrafa tabarbarewa, da ci gaba da ikonta na fifiko; abin da a yau ke ɗaya daga cikin muhimman abubuwan ƙarfin ƙasa.

Rabon Al’umma A Cikin Wannan Nasara

Idan za mu yi magana game da muhimmin abin da ya haifar da wannan nasara, dole ne mu yi nuni da rawar da jama'a suka taka. Babu wata ƙasa da ke wucewa manyan rikice-rikice kawai da kayan aikin soji ko ƙarfin tattalin arziki. Abin da ya sa Iran ta wuce wannan mataki shi ne jarin zamantakewa da jin nauyin da yah au kan daidaikun Al’ummar ƙasa da duk da matsin lamba, suka tsaya tare da ƙasarsu.

Wannan gaskiyar ita ce ta sa yawancin ayyukan kafofin yada labarai da ayyukan tunani suka zama marasa tasiri, kuma ya nuna cewa akwai rarrabuwar kawuna mai zurfi tsakanin rashin jin daɗin zamantakewa na al'ada da kuma haɗin kai da ayyukan waje.

Fara Sabon Babi

Duk da haka, zai zama babban kuskure idan muka ɗauki wannan lokaci a matsayin ƙarshen hanya. Nasarar da gaske tana tabbata ne lokacin da sakamakon tsayin daka ya zama ƙarfi mai dorewa; lokacin da haɗin kan ƙasa ya kiyaye, ƙarfin tattalin arziki ya ƙaru, jarin zamantakewa ya karu, kuma ƙwarewar wannan zamanin ta zama tushen tallafi ga makomar ƙasa.

Iran ta wuce tare da tsallake babbar jarabawa, amma muhimmancin wannan nasara ba wai kawai a cikin abin da ya faru ba ne; a'a, tana a cikin hangen nesa da aka buɗe wa ƙasar.

A yau, muhimmiyar gaskiya ita ce Iran ta ci gaba da wanzuwa; ba wai kawai ta ci gaba da wanzuwa ba, har ma ta soke yawancin hasashe da tsare-tsare da aka rubuta game da makomarta. Wannan shine batun da tarihi zai rubuta game da shi: al'ummar da ake tsammanin za ta mika wuya, ta tsaya tsayin daka; ƙasar da ake tsammanin za a raunana, ta ƙara ƙarfi; kuma mutanen da ake tsammanin za su gaji, sun nuna cewa har yanzu suna da ƙarfin gina manyan babi na tarihinsu.

Kuma watakila muhimmin saƙon wannan zamanin shi ne wannan; wannan ƙarshen yaƙi ne, ba ƙarshen hanya ba. Hanyar gaba, daga nan take farawa.

Rubutuwa: Editan ABNA

Fassarawa Da Yadawa: Babban Editan Sashen Hausa Na ABNA

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha