Kamfanin Dillancin Labaran Ƙasa Da Ƙasa Na Ahlul-Baiti (As) – Abna - ya bayar da rahoton cewa: Yemen a jiya a cikin tsarin hadin kan fagagen gwagwarmaya ta sanar a hukumance shigarta cikin fagen daga domin hana hare-haren Isra’ila kan Lebanon, kuma ta jaddada cewa Lebanon ba za ta kasance ita kaɗai a wannan yaƙin ba, kuma ba zai yiwu a raba wannan fagen dagar da sauran fagagen ba.
Dangane da rahoton jaridar "Al-Akbar" ta Lebanon, wannan matsaya ta fito ne a wata sanarwa daga Birgediya Janar "Yahya Sari" kakakin hafsoshin sojin Yemen. Ya ce hafsoshin sojin Yemen sun kai hari da makamai masu linzami zuwa cikin yankunan da aka mamaye kuma sun yi nasarar kai hari kan wasu muhimman wurare a Tel Aviv.
Sari ya kuma jaddada cewa sojojin Yemen za su kara martani yayin da aka tsananta rikici, kuma ayyukan soji kan Isr’aila za su fadada daidai da abubuwan da ke faruwa a fagen fama tare da hadin kai da ginshikin gwagwarmaya.
Kakakin sojojin Yemen a wani bangare na sanarwarsa ya sanar da rufe tekun maliya ga jiragen ruwan Isra’ila.
Ya bayyana cewa tun daga lokacin da aka fitar da wannan sanarwa, babu wani jirgin ruwa na 'yan kasuwa da wanda yake zuwa tashoshin jiragen ruwa na Falasdinu da aka mamaye da za a yarda ya wuce, kuma duk wani motsi da ke da alaka da Isra’ila a wannan yanki, zai zama halastaccen hadafin hari ga sojojin Yemen.
Yahya Sari a cikin wani sako ga Amurka da Isra’ila ya jaddada cewa sojojin Yemen ba za su yi shiru ba game da kewayen da aka yi wa al'ummar Yemen da al'ummomin tushen gwagwarmaya a Falasdinu, Lebanon, Iran, da Gaza.
Jimlar waɗannan abubuwan da ke faruwa suna nuna cewa Yemen tana ƙoƙarin tabbatar da wani sabon daidaito a yankin ta hanyar haɗa matsa lamba na soji, barazana ga jigilar kayayyakin Isra’ila a teku, da kuma goyon bayan Lebanon a fili. Wani daidaito wanda bisa ga shi, duk wani tsananta hare-haren Isra’ila a ɗaya daga cikin fagagen ginshikin gwagwarmaya, zai iya haifar da martani da ya wuce wannan yanki.
……………….
Your Comment