Taron Na Eidil Ghadeer Rana Ce Da Ake Tunawa, Wacce Manzon Allah (S.A.W.W) Ya Nasabta Dan'uwansa Imam Ali (A.S) A Matsayin Wasiyyinsa Kuma Magajinsa A Bayansa A Hajjin Bankwana. Taron Ya Gudana Ne A Muhallin Makarantar Fudiyyah Da Ke Babban Dodo Zariya. Inda Taron Ya Samu Halartan Daruruwan Ƴan Uwa Maza Da Mata Yara Da Manya Hadda Ma Tsofaffi. Tun Da Farkon Taron An Fara Ne Da Buɗewa Da Addu'a Da Kuma Karatun Alqur’ani, Sai Mawaƙa Suka Gudanar Da Wakokin Yabon Ahlul Baiti, Mawakan Wanda Suka Haɗa Da Yan Ɗariqa Masu Wakokin Imam Ali Na Ghadeer.
Bayan Kammala Waƙen Ne Aka Gabatar Da Tamsiliyya Nai Suna (Cin Amana ) Daga Bisani Kuma Wakilin Yan Uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) Na Da'irar Zaria Da Kewaye Wato Sheikh Abdulhamid Bello Ya Gabatar Da Jawabi. Bayan Kammala Jawabin Nasa Ne Aka Saurari Jawabin Jagora Sayyid Zakzaky (H) Na Ghadeer Wanda Ya Gabata A Wannan Shekarar. Bayan Kammala Sauraron Jawabin Ne Aka Yanka Alkaki, Aka Yi Sallolin Magrib Da Isha'i.
Daga Bisani Aka Yi Walima Aka Rufe Taron Da Addu'a. An Fara Taron Lafiya An Kuma Tashi Lafiya.
Zaria Media Forum
Your Comment