Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ma'aikatar Harkokin Wajen Hukumar Falasdinu, tare da fitar da wata sanarwa, ta yi Allah wadai da aikin yahudawa na kona masallatai biyu a ƙauyukan "Qasra" da ke lardin Nablus da "Kur" da ke lardin Tulkarm, kuma ta yi gargadi game da ƙaruwar hare-haren Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan.
Ma'aikatar a cikin wannan sanarwa ta jaddada cewa, waɗannan hare-hare suna faruwa ne tare da goyon bayan gwamnatin mamayar yahudawa kai tsaye. Wannan ma'aikatar ta jaddada cewa, hare-haren da ake yi akai-akai a kan wuraren ibada da dukiyoyin Falasdinawa, "Ayyuka masu haɗari" wadda ke buƙatar mataki na gaggawa na duniya don dakatar da shi.
Ma'aikatar ta sanar da cewa, laifukan da Yahudawa yan sheare guri zauna suke aikatawa a cikin tsari, ci gaba ne na manufofin tayar da hankali, goyon baya da tallafin gwamnatin mamaya a gare su, kuma ci gaba da siyasar bayar da kariya daga hukunci ga masu aikata waɗannan ta'addanci. Wannan ma'aikatar a cikin sanarwarta ta bayyana cewa, ci gaba da waɗannan tsare-tsare yana ƙara dagula yanayin fagen fama, kuma yana ƙara tsananta tashin hankali a Yammacin Kogin Jordan.
Ma'aikatar ta Falasdinu ta buƙaci al'ummar duniya da Majalisar Ɗinkin Duniya su ɗauki matakai "masu tasiri da tilastawa" don dakatar da hare-haren da gurfanar da masu aikata su, da kuma tabbatar da tsaron al'ummar Falasdinu da wuraren ibada. Wannan ma'aikatar ta jaddada wajabcin yunkurin al'ummar duniya don kawo ƙarshen ƙaruwar ta'addancin Yahudawan, da kuma hana ci gaba da ta'addanci a kan Falasdinawa, dukiyoyinsu da wuraren ibadarsu a yankuna daban-daban na Yammacin Kogin Jordan.
Kafin la'asar ranar Lahadi, garuruwa daban-daban na Yammacin Kogin Jordan sun shaidi yawaitar hare-haren soji na gwamnatin mamaya tare da ayyukan bincike da kama Falasdinawa, wanda ya zo daidai da ƙaruwar hare-haren matsuguna a kan gidaje, motoci, wuraren ibada da cibiyoyin fararen hula; yanayin da ke nuna tashin hankali da ba a taɓa yin irinsa ba tare da ci gaban na’urar yaƙin Isra'ila zuwa cikin Yammacin Kogin Jordan.
…………………
Ra'ayinka