6 Yuni 2026 - 13:01
Source: ABNA24
Yadda Gagarumin Taron Yaumul Ghadeer-Khum Ya Gudana A Garin Shado Birnin Gwari, Kaduna + Hotuna

Ƴan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) sun gabatar da gagarumin Taron Yaumul Ghadeer-khum a garin Shado da ke ƙaramar hukumar Birnin Gwari, Jihar kaduna.

Taron ya fara gudana ne da buɗewa da karatun Alqur'ani Mai Girma, sai IM Production suka yi  Tamsiliyya Mai taken 'Ranar Ghadeer-khum'. Tamsiliyya ta isar da sako sosai akan abinda ya shafi Miƙa wulaya Manzon Allah (SAWW) ga al'ummarsa.

Wakilin Yan uwa Musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (H) na garin Shado, Malam Abdulmumin Abubakar ya gabatar da Jawabi a Taron.

A karshe mawaƙa sun yi wakokin murna da ranar Ghadeer-khum, sai aka yi Addu'a aka tashi.

 An fara lafiya an kammala lafiya.

Daga Ammar .A. Shado

Zaria Media Forum

Your Comment

You are replying to: .
captcha