30 Mayu 2026 - 12:55
Source: ABNA24
Sayyid Zakzaky (H) Ga ‘Yan Uwa Ya Kamata A Kowace Ɗabi'a A Gan Mu Da Kyakkyawa

Wannan bayanin tsakure ne daga Littafin “TASIRIN ƊABI’U” na Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Wallafar cibiyar wallafa da yaɗa ayyukan Shaikh Zakzaky (H).

Jagora: “To ya kamata ya zama har wala yau an ga lallai 'yan uwa masu gaskiya ne, masu riƙon amana ne. Na san akwai wani rashin adalci da akan yi, na cewa idan wani mutum ɗaya ya yi wani abu, sai a ce ashe ma haka suke? Wannan zai zama rashin adalci. Don duk yadda aka kai ga gyaruwa, ba kuma duk gaba ɗaya kowa zai zama mizanin gyaruwansu ɗaya bane. Za a iya samun wani ɗan ɓata gari ko yaya, ko wani ya gaza ta wata hanyar. To amma idan ɗaya ya yi wani abu, to kuskure ne a yi hujumi a kan kowa. Amma in aka samu 'majoriti,' mafi yawa suna da wata siffa mummuna, ai siffarsu kenan. Don dama abin da ake yi a ma'auni in ka ji sau da yawa ana cewa ai waɗannan mutanen mutanen kirki ne ma'ana galibansu, in ka ji an ce ai ba mutanen kirki bane, ma'ana galibansu.

To ya kamata ya zama galiban 'yan uwa, galiban kuma mai rinjaye sosai. Kashi 95 zuwa 99 bisa ɗari, ya zama duk mutanen kirki ne. Nadiran ne za a sami wani; to ko da wani ya auna mu, ya ce mana ai an sami cikinku wani ya yi kaza, sai mu ce to ai ka ji dai ka ce wani ka samu a cikinmu, amma mu ba abin da muke yi ba kenan ai. Amma in aka sami 'majoriti' su ma 'yan Nijeriya ne, yadda Nijeriyawa suke Nijeriyancinsu haka su ma za su yi, to ka ga ko ma an samu sauyi Nijeriyanci za a ci gaba da yi.

Ka ga kenan ya kamata a kowace ɗabi'a a gan mu da kyakkyawa. Ko taro muka yi a ga cewa akwai tsafta a muhallin, a ga akwai natsuwa a muhallin, a ga akwai kiyaye komai a muhallin da sauransu. To wannan zai sa wato ya zama kenan sai mu sa fata kenan yana yiwuwa a samu…. Amma in aka gan mu, aka ga hayaniyarmu irin na 'yan Nijeriya, don 'yan Nijeriya an san su da hargowa. In ka je hajji ba ka bukatar a gaya maka 'yan Nijeriya. In ka ji ana ta hargowa, to sune. Sun fi kowa hargowa! Don su ko menene hayaniya kawai ake yi da faɗace-faɗace. To su kenan.

Na'am ba mune muka fi kowa mummunan abu ba, mutanen Misira sun fi 'yan Nijeriya sata. Sun fi kowa ma sata! Su suka shahara da sata. Kuma mutanen Yemen sun fi kowa wauta. Kuma 'yan Sudan ma sukan ɗan taɓa ɗan hargowa kaɗan, sai dai bai kai namu bane, da sauransu. To amma dai in ka ce hayaniya kam, da ma rashin tsafta, in ka ga ƙazanta ko'ina da ko'ina mune. To idan ya zamana su 'yan uwan da za su gyara 'yan Nijeriya su ma suna Najeriyanci, to Nijeriya tana nan. To ya kamata a ga bambamci ne.”

14/Zul-Hijja/1447

30/05/2026

Your Comment

You are replying to: .
captcha