Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: A cikin ayyukan hareh-haren da aka kai a kudancin Lebanon da arewacin Falasdinu da aka mamaye, an kai hari ga tankokin Merkava guda 5, inda tankoki 3 suka lalace suka kone ta hanyar jirage marasa matuki na Ababil, tanka daya da makami mai linzami, da wani tanka kuma da makami na musamman.
Dakarun Hizbullah na Lebanon sun yi nasarar kai hare-hare aƙalla ayyuka 22 a cikin sa'o'i 24 a kan matsugunan abokan gaba na Isra’ila, inda suka kai hari kan kayan yakin sojojin Isra’ila a yankin Al-Bayada da jirage marasa matuki na kunar bakin wake na Ababil.
Mayakan Lebanon sun kuma yi nasarar kai hari kan na’urar kakkabo makami mai linzami ta Iron Dome a yankin Ras Al-Naqoura da wadannan jirage. Wurin da sojojin Sahayoniyya suka tara da kayan aikinsu a Rashaf da Al-Bayada shi ma an kai masa hari da makamai masu linzami na Hizbullah.
…………………………….
Your Comment