30 Mayu 2026 - 11:50
Source: ABNA24
Afganistan: Mutane 18 Sun Mutu, 29 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Laghman

Sakamakon kifewar wata babbar mota da ke dauke da 'yan ci-rani da suka dawo daga Pakistan a lardin Laghman na Afghanistan, mutane 47 ne abun ya shafa jumullar wadanda suka mutu da jikkata.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa:  Abdul Malik Niyazi, kakakin gwamnan Laghman: hatsarin ya faru da safiyar yau a yankin Sorkhakan na gundumar Qarghayi a sakamakon hakan mutane 18 ciki har da yara 10 da mata 5 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 29 suka jikkata.

Wadanda suka jikkata a wannan hatsarin an kai su babban asibitin Nangarhar, kuma an fara bincike kan musabbabin faruwar hatsarin.

Haka kuma, Zabihullah Mujahid, kakakin gwamnatin Taliban, ya bayyana juyayinsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wannan hatsari. A cikin wani sakon nasa, ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa wadanda suka mutu, ya yi wa wadanda suka jikkata addu’ar samun waraka cikin gaggawa, ya kuma bai wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu hakuri da jimiri.

Wannan hatsari ya faru ne da misalin ƙarfe 5:30 na safiyar yau a kan babbar hanyar Kabul - Jalalabad, a cikin iyakar gundumar Qarghayi na lardin Laghman.

………………………………

Your Comment

You are replying to: .
captcha