Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Bayan martanin da Iran ta mayar kan harin da sojojin mamayar Amurka suka yi a wani wuri da ke gefen filin jirgin saman Bandar Abbas, ofishin hulda da jama'a na Rundunar IRGC ya fitar da wata sanarwa.
Ga cikakkiyar sanarwar:
Bismillahil Qasimil Jabbarin
_"Duk wanda yayi ta’adi akanku ku rama gwargwadon ta’adin da yayi maku akansa "_
بسم الله القاسم الجبارین
فمن اعتدی علیکم فاعتدوا علیه بمثل ما اعتدی علیکم
Bayan keta iyaka da sojojin Amurka masu mamaya suka yi a safiyar yau Alhamis, a wani wuri da ke gefen filin jirgin saman Bandar Abbas, ta hanyar amfani da makamai masu linzami na sama, an kai hari kan sansanin jiragen saman Amurka wanda aka harbor wannan harin daga gare shi, da ƙarfe 4:50 na safe.
Wannan martani ƙaƙƙarfan gargaɗi ne domin sanar da makiya cewa, keta iyaka ba zai kasance ba tare da an mayar da martani ba, kuma idan aka sake maimaitawa, martaninmu zai kasance mai tsauri, kuma alhakin sakamakonsa yana kan wanda ya fara kai harin.
و ما النصر الا من عندالله العزیز الحکیم.
_"Kuma babu wata nasara f ace daga wurin Allah, Mai ɗaukaka, Mai hikima"_
………………………………………………………….
Your Comment