Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Da sanyin safiyar yau Alhamis, mazauna yankin sun ba da rahoton jin karar fashewa a birnin Bandar Abbas.
Bisa ga wannan rahoto, ba a san ainihin dalilin wannan karar ba, kuma har yanzu babu wata cibiya a hukumance da ta bayyana ra'ayinta game da dalilin faruwar wadannan kararraki. Wasu rahotanni sun nuna cewa, rundunar tsaron sararin samaniya ta birnin Bandar Abbas ta fara aiki a cikin 'yan mintuna domin fuskantar makaman da ke kai hari.
Wani jami'in Amurka a cikin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce, sojojin Amurka sun harbo jiragen Iran marasa matuki waɗanda ke barazana ga sojojin Amurka da zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci a hanyoyin teku. Wannan jami'in ya kara da cewa: Sojojin Amurka sun kai sabbin hare-hare a kan wani wurin soji na Iran, wanda wannan wurin ya kasance barazana ga sojojin Amurka da tsaron zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hurmuz.
Your Comment