Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Gidan yanar gizo na Ibraniyawa "Hadshot Hamot" ya bayyana cewa sojojin Sahayoniyya sun ba da labarin kashe sajan "Rotem Yanay" wacce soja ce a bataliyar "Rotem" da ke karshin rundunar Go'ati.
Bisa ga wannan rahoto, wannan sojan Sahayoniyya ta mutu a ranar Laraba sakamakon fashewar wani jirgin mara matuki na kunar bakin wake da Hizbullah ta harba zuwa wani sansanin soji a garin "Shomra" a arewacin Falasdinu da ake mamayewa.
Haka kuma majiyoyin Ibraniyawa sun ba da rahoton cewa, wasu sojoji biyu daga sashin gaggawa na kibbutz a "Gorin" su ma sun jikkata a fashewar wani jirgin mara matuki.
………………………..
Your Comment