29 Mayu 2026 - 23:19
Source: ABNA24
Isra’ila A Ƙoƙarinta Na Kewaye Nabatiyah, Ta Shiga Cikin Tsaka Mai Wuya A Kudancin Lebanon

Sojojin Isra'ila suna ƙoƙarin yin amfani da kusurwar ƙauyen Zautar don kutsawa zuwa arewacin kogin Litani, ta hanyar mamaye wurare masu tsayi, suna son yin iko da bude wuta  a kan birnin Nabatiyah da sansanin "Ali Tahir".

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Sojojin Isra'ila suna ƙoƙarin yin amfani da hanyar ƙauyen Zautar don kutsawa zuwa arewacin kogin Litani. Isra’ila na yin waɗannan ayyukan soji, waɗanda ke tare da manyan hare-hare ta sama a ƙauyen da ke kewaye da Nabatiyah ne don ƙirƙirar wata "gada mai mahimmanci" don ƙarfafa matsayinsu a tattaunawar siyasa ko kuma faɗaɗa ikon sojinsu.

Wannan ci gaban ba a yi shi ta hankali kwance ba, sai dai sun tsara shi ne a matsayin dan ba don share hanyar zuwa gaɓar arewacin kogin Litani.

A gefe guda kuma, dakarun gwagwarmaya sun ɗauki dabarar saji cikin hikima, inda suka kai hari ga dabaru da kayan kariya na sojojin Isra'ila. Ayyukan dakarun gwagwarmaya ba su mayar da hankali ne kawai ga fuskantar manyan tankokin yaƙi ba, kai har sun lalata kayan aikin tallafi, na'urorin buɗe hanya (D9), tsarin sadarwa, da na'urar radar ta "Iron Dome".

Sakamakon a fagen daga ya nuna cewa, bayan kwanaki 86 da fara rikici, sojojin Isra'ila sun kasa ƙarfafa matsayinsu da gina shingen kariya, saboda yawan hare-haren da ake kai wa hanyoyin samar da kayayyakinsu da kuma haifar da kurumta a cikin hanyoyin sadarwar umarni.

Kididdigar yanayin fagen yaƙi a dukkan fagagen ta nuna cewa, dakarun gwagwarmaya sun yi nasarar mayar da abin da Isra'ila ta kira "fasaha" zuwa ƙalubale na dabaru da ma'aikata. Rashin sadarwa tsakanin rundunonin da ke yaƙi da dakunan umarni, da kuma ɓacewar garkuwar kariya, ya mayar da sojojin Isra'ila hadafin kai tsaye na dakarun gwagwarmaya.

A cikin yunkurinsu na zuwa birnin Tire, irin wannan gazawar da ta faru a wasu yankuna a baya ta tabbatar da cewa, rinjayen yakin sama da ƙoƙarin kafa katangar iyaka ba zai iya ba da tabbacin tsaron ma'aikatan soji ko mazaunan yankin arewa ba.

………………………………….

Your Comment

You are replying to: .
captcha