Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Ayyukan sun haɗa da kai hari kan tarukan motocin yaƙi da sojoji ta hanyar anfani da makamai masu linzami da jirage marasa matuki, baya ga haka kuma sun kai hari kan tankokin yaƙi na "Merkava" da motocin sulke na "Namera" a garuruwan: Al-Qusayr, Al-Adisa, Zoutar Al-Sharqiya, Al-Qantara, Arab Al-Luwaiza, Rashaf, Al-Bayada, Shama, Yahmar Al-Shqif, da Al-Malkiya.
Hizbullah ta jaddada cewa waɗannan ayyukan suna zuwa ne a cikin haƙƙin yin gwagwarmaya da mamaya da fatattakarsu. Ta kuma nanata cewa tana da alhakin kare ƙasarta da al'ummarta don hana abokan gaba ci gaba da manufofinsu masu haɗari ga Lebanon, ƙasarta, al'ummarta, da gwagwarmayarta.
……………………….
Your Comment