Sheikh Na'im: Za A Kiyaye Makaman Gwagwarmaya

Gwagwarmaya Sakamakon Jagorancin Shahidin Al'umma Sayyid Hassan Nasrallah Ne

Sheikh Na'im Qasim: "Gwamnati Ta Sauka Mana Idan Ta Kasa Tabbatar Da Shugabancinta".
25 Mayu 2026 - 08:31
Source: ABNA24
Gwagwarmaya Sakamakon Jagorancin Shahidin Al'umma Sayyid Hassan Nasrallah Ne

Babban Sakataren Hizbullah ta Lebanon a jawabinsa da ya yi dangane da bikin Gwagwarmaya da 'Yanci, ya bayyana cewa Gwagwarmaya sakamakon jagorancin Sayyid Shahidin Al'umma Sayyid Hassan Nasrallah ne. Ya kuma nanata adawarsa da batun kwace makamai, inda ya ce: "Har zuwa Lokacin da gwamnati za ta iya gudanar da ayyukanta, makamai za su ci gaba da kasancewa a hannunmu".

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul Bait (AS) - ABNA - ya ruwaito cewa: Sheikh Na’im Qasim Babban Shugaban Hizbullah Lebanon, a cikin jawabinsa dangane da ranar Gwagwarmaya da 'yanci, ya ce: "Duk wanda ya taka rawa a cikin Gwagwarmaya, yana da hannu a cikin 'yanci da nasarar da aka samu daga Gwagwarmaya".

Ya bayyana cewa Gwagwarmaya sakamakon jagorancin Shahidin Al'umma Sayyid Hassan Nasrallah ne, ya ce: "Nasarar ta samu ne sakamakon hadin gwiwa tsakanin sojoji, jama'a, da Gwagwarmaya ne".

Babban Shugaban Hizbullah ta Lebanon, yayi nuni da cewa ranar Gwagwarmaya ranar dukkan 'yan Lebanon ce da 'yantattun duniya kuma ranar Falasdinu ce, ya kara da cewa: "Hadakar gwamnati da Gwagwarmaya muhimmin abu ne kuma mai tasiri wajen samun 'yanci".

Ya ce: "Kada mu manta cewa hare-haren Gwagwarmaya sun tilasta wa makiya Sahayoniyya ficewa daga kasar Lebanon a shekara ta 2000 miladiyya".

Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa: "Soke yarjejeniyar kaskanci ta 17 ga Mayu a shekara ta 1984 wani mataki ne zuwa ga 'yanci". Ya ci gaba da cewa: "A shekara ta 2024 miladiyya, gwamnatin Lebanon ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta wadda ya kamata ta kawo karshen mamaya da cin zarafi na Sahayoniyya, amma a cikin watanni 15 da suka gabata, cin zarafi na Sahayoniyya ya ci gaba, kuma gwamnatin Lebanon ta kasa aiwatar da wannan yarjejeniya".

Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa: "Ba ma son gwamnatin Lebanon ta fuskanci aikin Amurka da Isra'ila, amma a kalla kar ta sauƙaƙe ma su shi".

Babban Shugaban Hizbullah Lebanon ya yi ishara da cewa: "Bayar da sassaucin da gwamnatin Lebanon ta yi ya kai ga har ta kai ga a ranar 2 ga Maris, 2026, aka dauki Gwagwarmaya wajen fuskantar gwamnatin Sahayoniyya a matsayin laifi".

Ya bukaci gwamnatin Lebanon da ta yi watsi da qudirorinta kan Gwagwarmaya, kuma ta kasance tare da jama'ar Lebanon.

…………………………………………………

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha