Yayi nuni da cewa muna da Gwagwarmaya mafi girma wadda ta kaskantar da makiya Sahayoniyya, ya na mai cewa: "Falasdinu za ta ci gaba da zama alkiblarmu, kuma za mu ci gaba da goyon bayan manufarta".
Babban Shugaban Hizbullah Lebanon ya ci gaba da cewa: "Iran karkashin jagorancin Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamenei shugaban juyin juya halin Musulunci, ta kaskantar da Amurka da gwamnatin Sahayoniyya".
Ya na mai ishara da cewa: "Iran za ta fito da nasara daga wannan yaki, kuma za ta zama a wannnan karon mai karfi wadda ke da matsayi na duniya, kuma za ta zama mafaka ga 'yantattu".
Your Comment