25 Mayu 2026 - 08:50
Source: ABNA24
Hizbullah: Ba Za Mu Taba Yarda Da Kwace Makaman Gwagwarmaya Ba

Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa: "Aikin Isra'ila shi ne ruguza Gwagwarmaya da mamaye Lebanon sannu a hankali." In da yayi ishara da cewa manufar takunkumin baya-bayan nan na Amurka shine matsa lamba kan Lebanon domin ramawa gazawarta wajen cimma burinta.

Ba Za Mu Taba Yarda Da Kwace Makaman Gwagwarmaya Ba

Ya kara da cewa: "Kwace makaman Gwagwarmaya a hakika kwace karfin tsaron Lebanon ne domin samar da fage ga ruguza kasar, kuma wannan al'amari ne da ba za mu taba yarda da shi ba".

Sheikh Naim Qassem, yana bayyana cewa gwamnati ce ke da alhakin kafa mulki da kuma kare kasar, ya nuna cewa: "Muna neman a dakatar da cin zarafin Sahayoniyya da ficewar wannan gwamnati gaba daya daga yankunan da ta mamaye na Lebanon, da 'yantar da fursunoni, da kuma dawowar 'yan gudun hijirar Lebanon zuwa gidajensu".

Ya kara da cewa: "Makamai za su ci gaba da kasancewa a hannunmu har sai gwamnatin Lebanon ta iya gudanar da ayyukanta."

Babban Shugaban Hizbullah  Lebanon ya bayyana cewa: "Abin da ke faruwa a yau shine tabbatar da tushen wanzuwar Lebanon a matsayin kasa mai karfi kuma mai 'yanci, da kuma fara rugujewar gwamnatin Sahayoniyya".

Za Mu Tsaya Tsayin Daka Wajen Fuskantar Duk Wanda Ke Tare Da Isra'ila

Sheikh Naim Qassem, ya nanata cewa Gwagwarmaya za ta ci gaba da kare kasa, jama'a, da mutuncin Lebanon, ya ce: "Duk wani bangare da ya yi fada da mu yana tare da gwamnatin Sahayoniyya, za mu tsaya masa tsayin daka".

Ya kara da cewa: "Asarori na hakika sun faru ga gwamnatin Sahayoniyya a kudancin Lebanon, saboda haka wannan gwamnati take kai hari kan fararen hula da gidajen jama'a. Jirage maras matuki na Gwagwarmaya na ci gaba da bin diddigin sojojin Sahayoniyya".

Babban Shugaban Hizbullah Lebanon, ya bayyana cewa keɓance makamai a hannun gwamnati a wannan mataki aikin Isra'ila ne, kuma ya kamata a yi watsi da shi, ya kara da cewa: "Idan gwamnati ba ta iya kafa mulki ba, to ya kamata ta tafi kawai".

Tattaunawar Kai Tsaye Da Gwamnatin Sahayoniyya Ba Ta Da Amfani

Ya kuma bayyana cewa: "Tattaunawar kai tsaye da gwamnatin Sahayoniyya ba ta da amfani, domin tana da riba ne kawai ga wannan gwamnati".

Sheikh Naim Qassem ya yi wa gwamnatin Lebanon magana da cewa: "Ku bar tattaunawar kai tsaye, kuma kada ku zartar da bukatun Amurka." Ya ce ku koma ga hadin kan kasa, domin ba tare da shi ba ba za ku samu wata nasara ba".

Babban Shugaban Hizbullah Lebanon ya ci gaba da cewa: "Muna fuskantar barazana, kuma a cikin irin wannan yanayi, sadaukarwa ce za ta gina makoma, domin muna son mu kasance masu 'yanci".

Ba Za Mu Taba Durkusawa A Gaban Gwamnatin Kisan Kiyashi Ta Sahayoniyya Ba

Ya ce: "Manufar wannan dukkan ta'addancin gwamnatin Sahayoniyya, kisa da ruguzawa shine don su durkusar da mu, amma ba za mu taba durkusawa ba, kuma za mu ci gaba da kasancewa a fagen fama, kuma za mu fito da nasara daga wannan yaki".

Sheikh Naim Qassem ya kara da cewa: "Za mu gina rugujarrun gidaje, kuma jama'armu za su koma gidajensu, kuma makiya da suka sha kashi za su fita daga Lebanon, kuma za mu shelanta 'yanci na uku".

Babban Shugaban Hizbullah Lebanon ya kuma ce Al’umma suna da hakkin hambarar da gwamnati domin fuskantar aikin Amurka da Isra'ila.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha