Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Bayanai sun nuna cewa hare-haren sun kuma fi mayar da hankali kan garuruwan Majdal Zoun, al-Mansouri, da Buyut al-Sayyad, kafin su sake dawowa da daddare tare da harbin bindigogi wanda ya shafi yankin al-Bayada, wanda ya shaida fafatawa da dakarun gwagwaramayar Musulunci na Hizbullah.
Har ila yau, sojojin Isra'ila sun harba bama-bamai masu haske a saman ƙauyukan sassan yamma da tsakiyar yankin, yayin da da sanyin safiya suka rushe wasu gidaje a unguwar al-Jabbana a cikin garin Bint Jbeil, a daidai lokacin da suke kai hare-haren manyan bindigu a gefen al-Ghandouriya.
A wani ci gaban fage na kuma, manazarcin gidan talabijin na Al-Manar ya ruwaito cewa wani jirgi mara matuki na Sahayoniya ya kai hari inda ya afka wa wata cibiya ta kasuwanci a kan hanyar al-Shihabiya - Kafrdounin, wanda ya haifar da asarar kayayyaki a wurin.
Your Comment