8 Mayu 2026 - 23:27
Source: ABNA24
Sojojin Iran: Makami Mai Linzami Guda 1 Da Jirage Marasa Matuƙa 3 Sun Sami Jiragen Ruwan Amurka

A sakamakon aikin haɗaka na makami mai linzami da jirage marasa matuƙa a aikin soji mai suna Shahid Mayvan, makami mai linzami (cruise missile) guda 1 da jirage marasa matuƙa na kunar bakin wake (suicide drones) guda 3 sun yi nasarar kai wa jiragen ruwan yaƙin Amurka da suka saba doka hari, lamarin da ya haifar da gobara akan jiragen.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sanar da cewa: "Da safiyaren Juma'a, ranar 18 ga watan Ordibehesht (daidai da 8 ga watan Mayu, 2026), a yayin da sojojin ruwan Amurka ke ƙoƙarin fitar da jiragen ruwan yaƙinsu guda 3 waɗanda suka saba doka, sun zo tare da taimakon jiragen samansu, daga mashigin Hormuz zuwa tekun Oman, sojojin ruwa na Iran sun kai wa wannan rukunin jiragen hari a wani aiki na haɗaka wanda ya ƙunshi makamai masu linzami guda 8 da jirage marasa matuƙa na kunar bakin wake guda 24."

Sakamakon wannan aiki, duk da yunƙurin da sojojin ruwan Amurka suka yi na kare kansu, makami mai linzami guda 1 da jirage marasa matuƙa guda 3 sun yi nasarar kai wa jiragen ruwan Amurka hari, inda suka haddasa gobara

Ya kamata a san cewa, an sanya wa wannan aiki suna "Shahid Mayvan" domin tunawa da kwamandan jirgin ruwan yaƙin Iran Jamaran, Kyaftin Amir Bahador Mayvan.

………………………………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha