9 Mayu 2026 - 18:29
Source: ABNA24
Lebonan Ta Zama Mayankar Sojojin Isra'ila

Wata jaridar Sahayoniya ta ruwaito cewa ƙasar Lebanan ta zama wani yanki mai cike da rikice-rikice da firgic ga sojojin Isra’ila, wanda hakan yana jawo wa gwamnatin Tel Aviv asara mai yawa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: aridar Ibrananci Maariv ta tabbatar da cewa a yanzu Labenan ta zama yanki mai tashin hankali da firgici ga sojojin Isra’ila, wanda hakan ke haifar da gwamnatin Sahayoniya asara mai girma.

Majiyoyi harshen Ibrananci sun ruwaito a ranar Juma'a game da wani lamari na tsaro da ya aukawa sojojin gwamnatin Sahayoniya a kudancin Lebonan, tare da kwashe sojojin da suka mutu da jikkata jirage masu saukar ungulu na gwamnatin.

Rahotanni na farko sun nuna cewa rundunar sojojin Sahayoniya ta fāɗa cikin kwanton bauna da mayakan Hizbullah suka shirya. Jirage masu saukar ungulu na sojojin Sahayoniya a sun ci gaba da aikin kwashe sojojin da suka jikkata ko mutuwa daga yankin da lamarin ya faru.

……………………….

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha