9 Mayu 2026 - 17:57
Source: ABNA24
Mutum 10 Sun Yi Shahada A Lebanon A Sabon Harin Da Isra’ila Ta Kai

Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa mutum 10 sun yi shahada yayin da wasu 20 suka jikkata a yau Asabar, bayan da sojojin Isra’ila suka kai hari a wasu garuruwa da ke kudancin ƙasar, wanda hakan ya zama sabon karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Majiyoyin labarai cikin gida sun bayar da rahoton cewa wuraren da wadanda sukai shahadar sun hada da garuruwan Az-Zrariyah, Aanqoun, Maifadoun, da Toura. Ya zuwa yanzu, ba a fitar da cikakken bayani game da lamarin ba.

Bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da aka kulla a farkon wannan shekara, Isra’ila ta sha karya wannan yarjejeniya a lokuta da dama. Wannan sabon hari ci gaba ne a jerin take hakkokin da Isra’ila ke yi duk da akwai dokokin kasa da kasa da aka amince da su.

Your Comment

You are replying to: .
captcha