8 Mayu 2026 - 09:36
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Na Cikin Shirin Ko Ta Kwana Bayan Kai Harinta Lebonan 

Yankunan da Isra'ila ta mamaye sun shiga cikin shirin ko ta kwana bayan harin da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa lebonan 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin sun kai hari da jirege marasa matuƙa a tsakanin garin Kafarshuba da Kafrahma da ke kudancin Lebanon a matsayin ci gaba da mamaye yankin Lebanon. 

A daya hannun kuma, tashar gwamnatin Sahayoniyya ta Channel 12 ta ruwaito majiyoyin na cewa gwamnatin na cikin shirin ko-ta-kwana a cikin yankunan da aka mamaye da kuma yankin kan iyaka saboda fargabar hare-haren da kungiyar Hizbullah za ta kai na martani. Majiyoyin Ibrananci sun kuma bayar da rahoton cewa, an soke ayyukan jama'a a yankunan da ke kan iyaka da Lebanon saboda yiwuwar kai hare-haren ramuwar gayya na Hizbullah.

Your Comment

You are replying to: .
captcha