9 Mayu 2026 - 18:11
Source: ABNA24
Guguwar Danniya Da Kame A Bahrain Kan Malaman Shi'a Da Al'umma

Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaron gidan sarautar Al Khalifa sun kai samame a gidajen malaman addinin Shi'a a Bahrain, inda suka yi bincike ba tare da wani takardar sammacin kotu ba, suka kama mutane da dama, suka kuma kwace wasu kadarorinsu na sirri.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: A safiyar yau jami'an tsaron gwamnatin Al Khalifa sun kai samame a gidajen malaman Shi'a a yankuna daban-daban na Bahrain, inda suka kama wasu malamai da dama. Masu lura da al'amura sun ce wannan wani bangare ne na danniyar tsarin mulki kan al'ummar Shi'a da kuma tsaurara matakan tsaro a tsakanin yanayin yankin.

Majiyoyin cikin gida da masu fafutuka a Bahrain sun ce jami'an tsaron sun shiga gidaje ba tare da izinin kotu ba, suka yi bincike, suka kame malamai da dama, tare da kwace wasu dukiyoyinsu na sirri. Duk da cewa gwamnatin Al Khalifa ba ta fitar da wani bayani a hukumance ba kan wannan mataki, amman majiyoyi a Bahrain sun ce an kama "daruruwan" malaman Shi'a, wadanda da dama daga cikinsu sun riga sun fuskanci tambayoyi, barazana, ko matsin lamba daga jami'an tsaro a baya.

Wannan mataki ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kame mutane da tsaurara matakan tsaro kan Shi'a a Bahrain tun bayan fara yakin da Iran ta yi. Kungiyoyin kare hakkin dan adam kamar Cibiyar Dimokuradiyya da 'Yancin Dan Adam ta Bahrain (BIRD) da Cibiyar Al-Amal sun ce a cikin watanni biyu da suka gabata an kama mutane sama da 200. A yau ma ma'aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ta yi ikirarin cewa ta kama mutane 41 da ake zargi da "alaka da dakarun juyin juya halin Iran (IRGC)". Ma'aikatar ta ce an kama "wata kungiya mai alaka da IRGC" ba tare da bayar da wata kwakkwaran hujja ba, kuma binciken ya shafi wasu wadanda ake zargi da nuna goyon baya ga hare-haren Iran.

Gwamnatin Al Khalifa a 'yan kwanakin nan ta kuma soke takardar  asalin zamowa dan kasa na mutane 69 da iyalansu, inda ta ce dalilin hakan goyon bayan Iran ne ko nuna jin dadin ayyukanta. Zarge-zargen da ake yi wa wadanda aka kama sun hada da "leken asiri ga IRGC", "cin amanar kasa", "yada bidiyoyin hare-haren Iran", "yabon ayyukan Iran", da "zuga tashin hankali". Masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce wadannan zarge-zargen an yi su ne da nufin danne 'yan adawa da kuma haifar da tsoro a tsakanin al'ummar Shi'a.

Your Comment

You are replying to: .
captcha