Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: UAE, tare da korar 'yan Pakistan 'yan Shi'a 15,000, da karɓe asusun banki da abin da suka samu na waɗanda suke zaune a wannan ƙasar da ke Tekun Farisa, sannan ta mayar da su ƙasarsu ta asali ba tare da suna da kuɗi a hannunsu ba.
Kamar yadda gidan talabijin na France 24 ya ruwaito, wannan mataki ya biyo bayan takun-saka tsakanin Abu Dhabi da Islamabad.
A dangane da haka, "Sorebhi Gupta" editan yankin kudu maso gabashin Asiya a mujallar New Lines, game da wannan batu ya ce: "A wannan mataki na ladabtarwa, UAE ta kori 'yan Pakistan 'yan Shi'a 15,000 waɗanda suka ɗauki wannan ƙasar da ke Tekun Fasha a matsayin gidansu tsawon shekaru ashirin da suka gabata".
Ya kara da cewa: "Da yawa daga cikin waɗannan mutanen da aka kora sun tafi UAE ne da burin samun aikin da ya dace, kuma ba tare da wani dalili ba aka kore su daga ƙasar. Da yawa daga cikin waɗannan mutanen sun gaya mani cewa an kai su wurin tsarewa, kuma ba tare da an ba su takardun shaidarsu ba, aka tura su jirgin sama zuwa Pakistan. Sun kuma ce UAE ta toshe asusun bankin su".
Your Comment