28 Afirilu 2026 - 22:22
Source: ABNA24
Wanene Al-Zaidi Sabon Firaministan Iraki?

Shugaban kasar Iraki a ranar Litinin ya nada Ali Faleh Kazem al-Zaidi tare umartarsa da ya kafa sabuwar gwamnati.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An yanke qudirin na da shi ne bayan yarjejeniyar "kwamitin tuntubar Ƴan Shi'a" da kuma samun goyon bayan mafi yawan wannan yunkurin siyasar. 

A cewar bayanan da aka wallafa, an haifi Al-Zaidi a lardin Dhi Qar kuma har yanzu bai rike wani muhimmin matsayi na siyasa a tsarin gwamnatin Iraki ba. Duk da haka, yana da bangarori daban-daban na kwarewa a fannin tattalin arziki, kudi da ilimi. 

Al-Zaidi, an haife shi a shekarar 1986 kuma shi ne dan takarar Firaminista mafi karancin shekaru a Iraki, da ya taba zama firaminista. Yana da digiri na farko a fannin shari'a, digiri na farko da na biyu a fannin kudi da banki; Haɗakar ilimin shari'a da tattalin arziki wanda manazarta suka ce zai iya yin tasiri wajen gudanar da lamurra da suka shafi mulki, zuba jari da ci gaban tattalin arziki. 

A cikin takardun bayanan Al-Zaidi akwai shugabantar hukumomi da ya ƙunshi cibiyoyi masu mahimmanci da yawa; Ciki har da Kamfanin Holandiq na Kasa, Jami'ar Al-Shaab, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Ashtar, da kuma Al-Masanub Bank, wanda ya sami gogewa wajen sarrafa bashi, saka hannun jari da batutuwa masu haɗari. Har ila yau, memba ne a kungiyar lauyoyin Iraki kuma ya shiga cikin batutuwan da suka shafi bunkasa tattalin arziki, sake fasalin tsarukan ilimi da mulki a cikin 'yan shekarun nan.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha