Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Rundunar Sojan Ruwa ta Irgc ta sanar da cewa: "Bisa sa ido kan leken asiri na IRGC a cikin watanni shida da suka gabata, jirgin ya yi zirga-zirga da yawa zuwa tashar jiragen ruwa na Amurka kuma an kama shi saboda yin watsi da gargadin sojojin ruwa da dama.
A wani ɓangaren kuma an samu rahotonnin da ke cewa har yanzu Iran tana lodi man a jiragen ruwa a tsibirin Kharak. Sabanin ikirarin da fadar White House ta yi, har yanzu babu bayyanar wata alamar ƙarewar karfin ajiyar man na Tehran.
Your Comment