24 Afirilu 2026 - 18:45
Source: ABNA24
Jiragen Marasa Matuƙan Hizbullah Su Na Da Kariyar Lantarki.

Jaridar Ibrananci Haaretz ta ba da rahoto game da kwarewar Hizbullah ta jiragen sama marasa matuka inda suka zamo kalubale ga gwamnatin sahyoniyawa.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Jaridar ta rubuta cewa jirage marasa matuka na Hizbullah ta ƙera jiragenta ne ta yadda ba zasu samu matsalar kutse na lantarki ba ko da abokan gaba sun so kakkaɓo su. 

Jaridar ta kara da cewa sabon yankin tsaro shi ma ba zai kawo cikas ga gudanar da ayyukan wadannan jiragen ba. Inda kwarewa da iyawar sojojin Isra'ila suka gaza don magance matsalar jirage marasa matuka FPV na Hizbullah. 

A cikin sabon zagaye na arangama, wani sabon nau'in jirgin kunar bakin wake maras matuki ya bayyana a fagen fama, wanda FPV Fiber optics ke sarrafa shi kuma ya kubuta tare da jure kai harin lantarki na Jaminak, jaridar Hebrew ta Hararetz ta ruwaito. Yin amfani da wadannan jirage marasa matuka na iya baiwa kungiyar Hizbullah damar shawo kan fifikon da majalisar ministocin sahayoniyya da jami'an tsaro suka yi fatan cimma ta hanyar samar da sabon tsarin kariyar tsaro a Lebanon.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha