22 Afirilu 2026 - 21:54
Source: ABNA24
ABNA: Ta Gudanar Taron Musamman Kan "Turkiyya Da Yaƙin Ramadan" + Hotuna

An gudanar da wani taro na musamman mai taken: "Turkiyya da Yaƙin Ramadan" a yammacin yau Laraba (22 ga Aprilu, 2026) bisa ga ɗaukar nauyin Cibiyar Zawia da Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: An gudanar da wani taro na musamman mai taken: "Turkiyya da Yaƙin Ramadan" a yammacin yau Laraba (22 ga Aprilu, 2026) bisa ga ɗaukar nauyin Cibiyar Zawia da Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA a zauren taron kamfanin dillancin labarai da ke Qom. 

A cikin wannan taron, Dr. Hassan Abdi, ƙwararre kan batutuwan Turkiyya da Caucasus, ya gabatar da bayani kan tasirin Yaƙin Ramadan akan zaman lafiyar cikin gida da na yanki na Turkiyya, Dr. Esmail Bandi Darya, ƙwararre kan batutuwan Turkiyya, ya gabatar da bayanin bincike kan nazarin matsayin hukuma da na wanda bana hukuma na Turkiyya kan Yaƙin Ramadan, Dr. Masoud Sadr Mohammadi, ƙwararre kan batutuwan Turkiyya, ya gabatar da bayani kan nazarin tasirin Yaƙin Ramadan akan al'ummar Alawiyya da ƙungiyoyin addini da ikilisiyoyi a Turkiyya, Dr. Hassan Sadeghian, farfesa a Jami'ar Tehran kuma darektan Cibiyar Zawia ta Turkiyya, ya gabatar da bayani kan tasirin Yaƙin Ramadan akan yanayin Musulunci na siyasa da matsayin masu tsattsauran ra'ayi a Turkiyya.

Hoto: Hamid Abedi

Your Comment

You are replying to: .
captcha