24 Afirilu 2026 - 18:30
Source: ABNA24
Iran Ta Mallaki Na'urorin Tsaro Na Zamani Da Iya Gano Dukkan Jiregen Yaƙi Da Kakkaɓo Su

Tsaron saman Iran yanzu ba ya amfani da radar ta gargajiya wanda hakan ya bayyana a ayyukan kakkaɓo jiragen Amurka da Isra'ila da sukai yunkurin kawo mata hari. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A wata hira da ABC, wani kanar sojan Amurka mai ritaya ya bayyana yadda Iran a yanzu ke amfani da tsarin radar daban-daban da ke yin barazana ga jiragen yaƙints nau'in F-35 yana mai cewa: Iran na amfani da tsarin infrared maimakon radar ta gargajiya. Wanda ba a tsara jiragen yaƙin Amurka irin su F-35 da F-15 don magance da ɓoye wa waɗannan tsarin kariyar ba. Filin sararin samaniyar Iran yanzu ba shi da aminci da tsaro ga nau'in jiragen yakin Amurka don haka dole sai dai ta yi amfani da wasu nau'in jiragen ko ta canja nau'in yanayin kai harin wanda wannan wani shan kaye ne na ƙarshe ga Amurka.

Your Comment

You are replying to: .
captcha