7 Afirilu 2026 - 13:52
Source: ABNA24
Mutane Uku Sun Mutu A Harin Bindiga Da Aka Kai Karimin Ofishin Jakadancin Isra'ila A Turkiya 

A harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Isra'ila a Istanbul mutane Uku sun mutu tare da jikkatar mutum ɗaya. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labarai sun bada rahoton cewa harbin da aka yi a Istanbul, kusa da karamin ofishin jakadancin gwamnatin Isra'ila a kawo yanzu dai an ba da rahoton cewa wani jami'in 'yan sanda ya jikkata sannan adadin wadanda suka mutu a ofishin jakadancin ya karu zuwa uku. 

An ce mutane uku sun tunkari karamin ofishin jakadancin Isra'ila da ke Istanbul a cikin wata mota, kuma daya daga cikinsu ya fara harbe-harbe daga nisan mita 70. Wani dan sanda ya jikkata a harin. Rahotanni daga kafafen yada labarai na Turkiyya sun bayyana cewa, mutane uku ne suka mutu a arangamar 'Yan sanda. 'Yan sanda sun rufe titunan da ke kaiwa ofishin jakadancin.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha