7 Afirilu 2026 - 00:15
Source: ABNA24
An Sanar Da Yadda Za'a Gudanar Da Tarukan Ranar 40 Shahadar jagoran Juyin Juya Halin Musulunci

Majalisar da ke kula da Yaɗa Lamurran Musulunci ta sanar da yadda za gudanar da tarukan juyayi na kwana 40 da shahadar jagoran juyin juya halin musulunci ga al'ummar kasar, ta mai gayyatar dukkan sassan al'ummar wannan kasa mai girma da su sake haifar da wani yanayi na al'ajabi mai dorewa. 

Nassin sanarwar da majalisar ya kasance kamar haka: 

Da sunan Allah mai rahama, Mai Jinkai. 

بسم الله الرحمن الرحیم.

وَلَا تَحسَبَنَّ الَّذِينَ قتِلوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ یرزَقونَ. 

Kwanaki arba'in sun shude da faruwar mummunan lamari al'ummar musulmi suke cikin juyayi da jimamin rashin babban ɗan Husain Ibn Ali, sun zauna makoki mafi daci a tarihinsu na zamani. Ayatullahil Uzma Ayatullah Imam Sayyid Ali Husain Khamenei (Allah ya ƙara tsarkake ruhinsa) - babban shugaba jagoran al'ummar musulmi, shugaba kuma shugaban musulmin duniya, limamin masu 'yanci da wanda aka zalunta, abin koyi na Ijtihad, jihadi da juriya maɗaukin tuta.

A cikin wani mummunan hari da 'yan ta'addar Amurka da Isra'ila, Sayyid ya yi shahada kuma ruhinsa ya ta shi zuwa Malakutil Aala. 

Limamin mai hikima ya sadaukar da rayuwarsa mai albarka wajen inganta kalmar gaskiya, da kare juyin juya halin Musulunci, da hidima ta gaskiya ga wannan al'umma mai girma. Al'ummar da a cikin kowane ma'auni na tarihi suke nuna dangantakarsu da alaƙardu mai zurfi ga marigayin shahidin.

A yanzu, a ranar arba'in da hawan ruhinsa ga malakutil Aala, tare da halartarku mai ban mamaki da ke yankewa makiya fata, da zai tabbatar da cewa ba wai kawai za ku zubar da hawaye cikin makoki ba ne ga limaminku, sai dai zaku tsaya tsayin daka kan daɗaɗɗen alkawarinsa da kuma tsayuwar alkawarinsa akan tafarkinsa da manufansa, kuma a halin yanzu, tausayawar Allah ne da hikimar Allah wanda a lokacin wannan makoki, ta hanyar zabar magaji mai adalci da kuma Magaji mai cancanta, Ayatullahil Uzma Imam Sayyid Mujtaba Khamenei (Allah ya tsawaita Rayuwarsa cikin kulawarsa)...

Za'a Gudanar Da Tarukan ne kamar haka: 

Rana Laraba, wanda ya zo daidai da daren shahada na 40, za a gudanar da tarukan makoki, da tarukan bugun kirji a gungu-gungu, da tarukan waƙoƙin juyayi, tunawa da bala'i da masibobi da karatun Alkur'ani a dukkan manyan Mayadin, Masallatai da wuraren ibada masu tsarki a fadin kasar daga karfe 8 na dare.

 A ranar Alhamis, wanda yayi daidai lokacin da shahadar Shahid Jagoran Al'umma da karfe 9, za'a gudanar da tattaki makoki na na gungu-gungun kungiyoyin makoki da tawagogin addini daga dandalin Jomhuri Eslami zuwa wurin da ke fuskantar wurin da Jagora yayi shahada, wato titin Dost Khiyaban Kishvar Doost, wanda ke kan titin Jomhuri, Tehran. Har ila yau, za'a gudanar da addu'ar Imam Zaman (AS) da muryar Jagoran juyin juya hali da karfe 9 na dare a cikin mayadin da wurare masu tsarki.

A ranar juma'a kuma daga karfe goma na safe a lokaci ɗaya da wuraren sallah na dukkan ƙasar za'a gudanar da tarukan juyayi da girmamawa da tunawa da jagora Shahid inda za'a gudanar da wasu tsaruka kamar karatun Alkur'ani da addu'a ta 14 da ke cikin Sahifah Sajjadiyyah da kuma waƙoƙin jaje daga mawaka.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha