28 Maris 2026 - 14:21
Source: ABNA24
Iran: Dakarun Irgc Na Ci Gaba Da Kama Ƴan Leƙen Asirin Maƙiya

Cikin ƴan kwanakin nan an kama sama da ƴan leƙen asirin maƙiya sama da 150 a sassan ƙasar Iran 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Sojojin Imam Zaman da ba a bayyana sunansu ba a cibiyar leken asiri ta Furaj na lardin Mazandaran, tun daga farkon yakin Ramadan ta hanyar sarrafawa da sa ido kan matakan leken asiri da fasaha na abokan gaba, sun yi nasarar ganowa da kama mutane 50 da suka tuntubi tare da alaƙa da Cibiyar watsar labarai ta a abokan gaba wato IranInternational kafar Man Wa To. Waɗannan mutane suna aiki don aika bayanai da ƙayyadaddun bayanai masu alaƙa da tsaro da wuraren soja a lardin. 

Sannan ofishin Hulda da Jama'a na Kashan: an kama ɗaya daga cikin jami'an zagon kasa da suka ba da hadin kai da cibiyoyin 'yan adawa na kasashen waje an gano shi tare da kama shi bisa umarnin mai gabatar da kara na Kashan. Har ila yau, an kama wasu ‘yan zagon ƙasa biyu munafukai tare da tura su gidan yari a lokacin wani harin ba-zata. 

Sannan an kama Mambobin kungiyar leken asiri ta Mossad guda 3 da ke Kermanshah bisa kokarin sojojin Imam Zaman (AS) da ke rundunar Nabiyul Akram (SAW) a Kermanshah. Tawagar 'yan ta'addan mai ɗauke da mutane uku, karkashin jagorancin jami'an hukumar leken asiri ta Sahayoniyya, sun yi yunkurin tayar da hankali akan tituna da kuma haifar da aikin ta'addanci a wurare masu mahimmanci na tsaro, amma sojojin Imam Zaman (AS) da ke kungiyar leken asiri ta IRGC sun gano su tare da kama su. 

An samu manyan makamai a wajen wadannan mutane, da harsasai masu yawa, da na'urorin da ake amfani da su wajen kera harsasai. 

Cibiyar leken asiri ta IRGC ta bukaci jama'a da su kai rahoton duk wani batu da suke shakka akan sa ga wannan number 114. 

Sannan an kama sojojin haya na cikin gida 15 a Isfahan bisa ayyukan leken asiri na sojojin Imam Zaman (AS) sojojin haya 15 na Cibiyoyin ta'addanci na IranInternational da kafar Manoto (Hedkwatar Watsa Labarai ta Isra'ila) wadanda suke aikawa da hotunan hare-haren bama-bamai na Sahayoniya-Amurka da kuma da wuraren sojoji, wuraren masu aikin ceto, da wuraren bincike a kan hanya da sauransu. 

An kuma gano da kama jami'an haya 51 da jami'an ta'addanci a Ilam. Daga cikin mutane 51 'yan hayar ta'addanci da aka kama, 5 bisa zargin shirya tarzomar kan tituna da haifar da rashin tsaro, 2 bisa zargin kokarin da shirin haifar da cunkoson ababen hawa, 10 bisa zargin ɗaukar hotuna ga wuraren soja da wuraren zama na soja. An kuma shigar da kara a kan mutane 19 kan zargin alaka da hada kai da cibiyoyin sadarwar masu adawa da suka hada da Cibiyar ta'addanci IranInternational, an kuma kama mutane 15 da suke yin kokarin kawo cikas ga tarukan dare na jama'a don nuna goyon baya ga gwamnatin. 

Wadannan matakan leken asirin sun dogara ne akan rahotannin jama'a kuma an bukaci dukkan Al'umma masu daraja da suyi taka tsantsan a lardin da su gaggauta bayar da rahoton duk wani aiki da ake tuhuma ga number 114 ta Cibiyar leken asiri ta lardin. 

An gano tare da kama jami'an hayar dake leken Asiri ga Amurka da Sahayoniya 8 a yammacin Azerbaijan.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha