Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Al-Manar ta ruwaito a cikin wani rahoto da ta fitar a sanarwa ta bakwai ta kungiyar Hizbullah daga safiyar yau cewa, Hizbullah na gudanar da yaki kai tsaye gaba da gaba fuska da fuska da sojojin Isra'ila a kudancin birnin Al-Kiyyam na kudancin Lebanon.
Hizbullah a bayana ta ta fira cewa: "A cikin ayyukan kariya ga tsaron Lebanon da al'ummarta, mujahidai gwagwarmayar Musulunci sun shiga fada kai tsaye da gaba da gaba da sojojin abokan gaba na Isra'ila a birnin Al-Kiyyam da makamai masu nauyi da rokoki har zuwa karfe 10:00 na safiyar yau Asabar.
Kungiyar Hizbullah ta sanar a cikin sanarwarta ta shida: Da karfe 6:30 na safiyar yau, mujahidan Musulunci sun kai hari wurin taruwar sojoji da ababen hawa na Isra'ila a yankin Al-Tayba da makami mai linzami na musamman.
Kungiyar Hizbullah ta sanar a cikin sanarwarta ta hudu da biyar da Karfe 6:20 na safiyar ranar Asabar, ta kai hari kan sojojin Isra'ila da motocin soji a yankin Khala al-Aqsa da ke kan iyaka da garin Al-Adisa da Meika. Mujahideen na gwagwarmayar Musulunci sun yi arangama da sojojin Isra'ila a lokacin da suke kokarin kutsawa da yankin Al-Tabasin zuwa ginin karamar hukumar na garin Al-Naqura, kuma sun yi amfani da makamai masu nauyi da kananan makamai a kansu, wadanda suka yi sanadin asarar rayukan Isra'ilawan.

Kungiyar Hizbullah daga safiyar yau, da karfe 10:45, dakarun wannan yunkuri sun kai hari wurin taron sojojin Isra'ila a kusa da gidan yarin Al-khayyam da makamai masu linzami. Mujahidan kungiyar gwagwarmayar Musulunci sun yi ruwan makamin roka a sansanin Filon da ke kudancin yankin Rosh-e-bina. Sannan Hizbollah ta kuma gudanar da ayyuka 55 a hare-harenta kan Isra'ila a kudancin Lebanon da kuma tsakiyar yankunan da aka mamaye a jiya.
Ra'ayinka