11 Maris 2026 - 16:39
Source: ABNA24
An Gudanar Da Taron Girmama Shahid Imam Khamenei A Tanzaniya + Hotuna

Bisa halartar mabiya addinai da mazhabobi daban-daban An gudanar da taron tunawa da Marja’ul A’ala Ayatullahil Uzma Imam Sayyid Ali Husini Khamenei (Qs) a Jami'ar Mustafa Tanzaniya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): An gudanar da taro mai dinin yawa da muhimmanci don tunawa da Shahid masanin shari'a Mujahidi, Malamin Allah jagoran Al'ummar Musulunci, Sayyid Ayatullah Sayyid Ali Husaini Khamenei (Qs), tare da halartar dimbin malaman addini da kimiyya da al’adu a jami’ar Mustafa Tanzania.

A cikin wannan taro na ruhaniya da daukaka, gungun fitattun jami'ai da mutane, ciki har da jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Tanzaniya, mai ba da shawara kan al'adu na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, darektan Al-Mustafa, malaman Shi'a da malaman Sunna, Kiristoci, malaman jami'a, Dalibai, ɗaliban ilimin addini da ƙungiyar membobin al'ummar Khoja Isna Ashriyya sun halarta kuma ta hanyar halarta cikin wannan taron ibada, sun girmama tunawa da wannan babban jagora na duniyar Musulunci. An fara bikin ne da karatun wasu ayoyi kadan daga Alkur'ani mai girma, sannan masu yabon Ahlul Baiti (SAW) suka waken jajentawa da nuna bakin ciki inda suka karanta fatiha da yin addu’oi cikin juyayi.

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha