Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kafofin yada labarai na sahyoniya sun ruwaito cewa: A wani hari na baya-bayan nan zuwa tsakiyar Isra'ila, kungiyar Hizbullah ta harba makamai masu linzami a karon farko, inda mutane da dama suka jikkata. An bayar da umarnin yin shiru kan wannan lamarin. A wani ɓangaren kuma Kungiyar Hizbullah ta sanar da kai hari kan kayayyakin ayyukan sojojin Isra'ila a kudancin Lebanon.
Hizbullah ta kai hari kan wata motar bulldozer da motoci biyu na sojojin abokan gaba na Isra'ila a tsaunukan Al-Qaba.
Your Comment