9 Faburairu 2026 - 21:46
Source: ABNA24
IRGC: Shankayen Makiya A Jere Na Nuni Da Iko Da Takatsantsan Al’ummar Iran Ne

Sanarwar IRGC Kan Bikin Cika Shekarun Nasarar Juyin Juya Halin Musulunci; Kayar da Makiya Suka Yi a Jere Alama Ce Ta Iko da Kulawar Al'ummar Iran

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): A cikin wata sanarwa bisa munasabar bikin cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin Musulunci, IRGC ta fitar da sanarwa inda a ciki ta ke cewa: shankayen da makiyan Iran suka yi a jere a cikin shekaru 47 da suka gabata, ciki har da gazawar Amurka da gwamnatin Sahyuniya a cikin yaƙe-yaƙe da tarzomar baya-bayan nan, kuma ta dauki wadannan ci gaba a matsayin wata alama ta rashin fata na masu girman kan duniya, kuma ta jaddada cewa Jamhuriyar Musulunci, wacce ta dogara da gogewar shekaru arba'in na juriya da gwagwarmaya, tana da ingantacciyar kariya, shirye-shiryen aikin kai hari da kariya, da kuma cikakken liken asiri ingantacce.

Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da yunkuri Pahlawii kuma ta tayi ishara da rawar takunkumi da sakamakon da ya haifar a lokacin dogaro da kasashen waje suka taka a cikin kalubalen yau, sannan ta jaddada sabunta alkawari ga manufofin juyin juya halin da biyayya ga shugabanci ta hanyar girmama tunawa da Imam Khomeini (RA) da shahidan juyin juya halin da tsaro, sannan ta gayyaci al'ummar Iran da su shiga cikin tattakin da za’a gudanar a duk fadin kasar a ranar 22 ga Bahman wanda za’a gudanar ranar Laraba mai zuwa 11 ga watan Fabrairu 2026.

Your Comment

You are replying to: .
captcha