2 Faburairu 2026 - 22:00
Source: ABNA24
Rahoton Yadda 'Yan Tsirarun Shi'a Na Afghanistan Ke Rayuwa A Cibiyar Rashin Tsaron Ta Taliban Da ISIS

Wani rahoto na musamman daga Kamfanin Dillancin Labarai na "Baggasht" ya nuna cewa rashin tsaro da aka tsara shi ga 'yan Shi'a na Afghanistan ya samo asali ne daga tsarin ta'addanci tsakanin Taliban, ISIS Khorasan, da Tehreek-e-Taliban Pakistan; kungiyoyin da ake raba hare-hare, ƙirƙirar labarai, da kuma karɓar alhakin da gangan tsakanin waɗannan ƙungiyoyi.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA): Kamfanin Dillancin Labarai na Baggasht ya sanar a cikin wani rahoto na nazari cewa tsirarun Shi'a na Afghanistan sun kasance hadafin hare-hare ga wani tsararren tashin hankali a cikin 'yan shekarun nan wanda ya wuce ayyukan ta'addanci na lokaci-lokaci da ya samo asali ne daga haɗin gwiwar aiki da kafofin watsa labarai tsakanin Taliban, ISIS Khorasan, da Tehreek-e-Taliban Pakistan.

A cewar sakamakon wannan rahoton, hare-haren da aka kai wa 'yan Shi'a na Afghanistan, wadanda suka hada da bama-bamai a makarantu, jami'o'i, masallatai, cibiyoyin lafiya, da kuma tarukan fararen hula, galibi ana kai su ne ta hanyar wasu mutane da ke da alaƙa da Taliban, amma sai ISIS-K ta dauki alhakin hakan a kafofin watsa labarai.

Wannan tsari ya bai wa Taliban damar bayyana cewa ba su da laifi wajen kashe fararen hula, yayin da suke ci gaba da haifar da tsoro da kawar da tsirarun yan Shi’a.

Rahoton ya jaddada cewa 'yan Shi'a na Afghanistan, musamman 'yan Hazaras, su ne a tsakiyar hadafin akidar wannan kungiyar ta'addanci saboda imaninsu na addini.

Ra'ayoyin takfiri da suka yadu a tsakanin Taliban, ISIS, da Taliban na Pakistan sun dauki 'yan Shi'a a matsayin "masu ridda" da "wanda jininsu ya halatta," kuma wannan ya share fagen ci gaba da tashin hankali da ya bazu a kan wannan tsirarun mabiya addinin.

Idan muka koma ga labarin, wannan tsarin ta'addanci, wanda aka fara kafawa a Afghanistan, yanzu haka an mayar da shi zuwa Pakistan; Inda Kungiyar Taliban ta Pakistan, tare da hadin gwiwar ISIS Khorasan, ta sake buga irin wannan tsarin da "wata kungiya ta kai hari wata kungiyar ta dauki alhakin."

Manufar wannan tsari ita ce rage kashe kuɗi a siyasa da zamantakewa, tsaftace fuskokin wasu masu ruwa da tsaki, sannan a lokaci guda, ci gaba da kawar da tsirarun da aka yi niyya.

Wani ɓangare na rahoton ya bayyana cewa Afghanistan a ƙarƙashin mulkin Taliban ta zama mafaka mai aminci ga ayyukan ta'addanci da haɗin gwiwar leƙen asiri daga waɗannan ƙungiyoyi, wanda ya ƙara ta'azzara yanayin tsaro na tsirarun addinai, musamman 'yan Shi'a.

A cewar masu lura da tsaro, matuƙar ba a amince da wannan haɗin gwiwar 'yan ta'adda da kuma tsarin raba aiki tsakanin Taliban, ISIS Khorasan, da Ƙungiyar Taliban ta Pakistan a matsayin barazana ɗaya tilo ba, za a ci gaba da samun rashin tsaro da kashe 'yan Shi'ar Afghanistan, kuma waɗanda abin ya shafa za su yi shiru a inuwar labaran ƙarya da kuma canzadaukar nauyi na ta’addanci da akai masu.

Your Comment

You are replying to: .
captcha