9 Mayu 2026 - 23:28
Source: ABNA24
Me Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Turai Da Isra’ila Ta Kunsa? Me Yasa Aka Dakatar Da Ita Ya Zama Mai Wahala?

Yayin da matsin lamba na siyasa da na kare hakkin bil'adama ke karuwa kan gwamnatin Sahayoniya, batun dakatar da yarjejeniyar haɗin gwiwar Tarayyar Turai da Isra'ila ya sake zama kanun labarai.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya ruwaito cewa: Matsin lamba na siyasa da na kare hakkin bil'adama a cikin Tarayyar Turai don dakatar da yarjejeniyar haɗin gwiwa da Isra'ila yana karuwa bayan zarge-zargen da ake yi wa Tel Aviv game da take hakkin bil'adama da dokokin kasa da kasa a Zirin Gaza, Yammacin Kogin Jordan, da Lebanon. Amma wannan tsari ya gamu da cikas mai sarkakiya na tattalin arziki da siyasa, wanda hakan ya sa yanke shawara a kai ya zama mai wahala.

A cewar rahoton tashar Al Jazeera a watannin baya-bayan nan, kasashe kamar Spain, Ireland, da Slovenia sun bukaci a sake duba ko kuma a dakatar da wannan yarjejeniya. Akasin haka, kasashe kamar Jamus da Italiya sun ki amincewa da daukar tsauraran matakai kan Isra'ila. Wannan rashin jituwa yana nuna cewa Turai ta shiga tsaka-tsakin tsakanin la'akarin kare hakkin bil'adama da muradunta na tattalin arziki da siyasa.

Rashin jituwa bai tsaya ga sashi na biyu na yarjejeniyar ba - sashen da ya sharɗanta ci gaban dangantakar bangarorin biyu bisa mutunta hakkin bil'adama da ka'idojin dimokradiyya. Babban batu shi ne, tsadar siyasa da tattalin arziki na dakatar da yarjejeniyar da ta zama wani muhimmin sashi na tsarin dangantakar tattalin arziki da fasaha tsakanin Turai da Isra'ila tun daga shekara ta 2000.

Bisa ga bayanan Hukumar Tarayyar Turai, Isra'ila ita ce abokiyar ciniki ta 51 a Tarayyar Turai, kuma tana da kusan kashi 0.8 cikin 100 na jimillar cinikin kayayyaki na Turai da duniya. A gefe guda, Tarayyar Turai ita ce babbar abokiyar cinikin Isra'ila, kuma tana da kusan kashi 32 cikin 100 na jimillar cinikin kayayyaki na wannan gwamnati da duniya - lamarin da ke nuna irin dogaron da tattalin arzikin Isra'ila ke da shi ga kasuwar Turai.

Yawan cinikin kayayyaki tsakanin bangarorin biyu a shekara ta 2024 ya kai kusan Yuro biliyan 42.6. A wannan lokacin, Tarayyar Turai ta shigo da kayayyaki daga Isra'ila na Yuro biliyan 15.9, kuma ta fitar da kayayyaki na Yuro biliyan 26.7 zuwa Isra'ila - adadi da ke nuna rarar ciniki na Yuro biliyan 10.7 ga Turai.

Amma Me Sassan Yarjejeniyar Haɗin Gwiwar Turai Da Isra'ila Ya Kunsa?

Yarjejeniyar haɗin gwiwar Turai da Isra'ila ita ce babban tsarin shari'a na dangantakar bangarorin biyu, wanda aka sanya hannu a Brussels a shekara ta 1995 kuma aka fara aiwatar da shi daga watan Yuni na shekara ta 2000. Wannan yarjejeniya ta ginu a kan kafa yankin ciniki cikin 'yanci sannu a hankali, bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki, kasuwanci, kimiyya da fasaha, da kuma tattaunawar siyasa tsakanin bangarorin biyu.

Dangane da wannan yarjejeniya, Isra'ila ta sami damar shiga kasuwar Turai cikin fifiko, kuma an rage ko kawar da yawancin takunkumi da harajin kwastam kan kayayyakinta. Haka kuma, an kulla jerin yarjejeniyoyin kari a fannonin kamar kayayyakin noma, magunguna, sufurin jiragen sama, da dokokin asalin kayayyaki tsakanin bangarorin biyu.

Dokokin asalin kayayyaki suna bayyana a wace ƙasa aka kera wani samfuri, da ko ya cancanci yafiyar haraji ko sassauci a cinikayya.

Wani muhimmin sashi na hadin gwiwar tsakanin bangarorin biyu shi ne yarjejeniyar "Bude sararin Sama" wadda ya rage takunkumin zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasashen Turai da Isra'ila, kuma ta samar da damar fadada sufurin jiragen sama da karin gasa a kasuwar tikitin jirgi.

Me yasa wannan yarjejeniya ke da mahimmanci ga Isra'ila?

Muhimmancin wannan yarjejeniya ga Isra'ila bai tsaya ga fitar da kayayyaki kawai ba. Tarayyar Turai ita ce babbar kasuwar fitar da kayayyaki, kuma daya daga cikin manyan hanyoyin shigo da kayayyakin masana'antu, fasaha, da zuba jari ga tattalin arzikin Isra'ila.

Bisa ga kididdigar Hukumar Tarayyar Turai, a shekara ta 2024, kusan kashi 34.2 cikin 100 na shigo da kayayyakin Isra'ila daga Turai ya kasance, kuma kashi 28.8 cikin 100 na fitar da kayayyakin ta ya tafi kasuwar Turai ne.

Wani muhimmin sashi na fitar da kayayyakin Isra'ila zuwa Turai ya hada da injina, kayan sufurin jiragen sama, sinadarai, kayan kimiyya da lantarki, da kayayyakin fasaha na zamani. Haka kuma, hadin gwiwar kimiyya, fasaha, kirkire-kirkire, da sarrafa albarkatun ruwa suna daga cikin manyan abubuwan amfanin wannan yarjejeniya ga Isra'ila.

Masana tattalin arziki sun yi imanin cewa wannan yarjejeniya ga Isra'ila ba kwangilar ciniki ce kawai ba, sai dai ta zamo wani sashi mai mahimmanci na tsarin tattalin arzikin wannan gwamnati, musamman a fannin fasahar zamani da jawo hankalin zuba jari daga waje.

Wace Riba Turai Take Samu Daga Wannan Yarjejeniya?

Ko da yake Isra'ila ta dogaro da Turai ne, amma Tarayyar Turai ma tana samun riba mai mahimmanci daga wannan yarjejeniya. Turai, baya ga samun rarar ciniki, tana da damar shiga kasuwar masu amfani da manyan kudin shiga, kuma tana hada kai da Isra'ila a fannoni kamar tsaro intanet, makamashi, magunguna, da fasaha.

Fitar da kayayyakin Turai zuwa Isra'ila ya hada da injina, kayan sufurin jiragen sama, sinadarai, da kayayyakin masana'antu. Wasu kasashen Turai kamar Spain suma suna daga cikin manyan masu fitar da motoci zuwa Isra'ila.

Duk da haka, masana tattalin arziki sun ce illar da Turai za ta iya fuskanta idan aka dakatar da yarjejeniyar za ta zamo kasa da illar da Isra'ila za ta fuskanta, saboda Tarayyar Turai tana da wasu kasuwanni da za su iya maye gurbinsu, da kuma karfin tattalin arziki mafi fadi.

Menene Zai Faru Idan Aka Dakatar Da Yarjejeniyar?

Masana sun yi imanin cewa dakatar da yarjejeniyar gaba daya ko sashi-sashi na iya haifar da sakamako kai tsaye da kuma sakamako a kaikaice ga tattalin arzikin Isra'ila.

A matakin kai tsaye, akwai yiwuwar karin harajin kwastam, wahalar shigar da kayayyakin Isra'ila zuwa kasuwar Turai, da kuma sarkakiyar dokokin ciniki.

Amma illolin kaikaice, kamar su lalata sunan Isra'ila a matsayin abokiyar ciniki da aka amince da ita, kara hadarin zuba jari, matsin lamba kan kamfanonin fasaha, da raguwar karfin jan hankalin zuba jari daga waje, na iya zama mafi tsanani.

Masana sun kuma yi gargadi cewa irin wannan yanke kudiri na iya isar da sako mai muhimmanci ga kasuwannin duniya – sakon kuwa shi ne cewa dangantakar Isra'ila da babbar abokiyar cinikinta ba ta cikin kwanciyar hankali kuma - lamarin da zai iya shafar ci gaban tattalin arziki, darajar bashi, da amincewar masu zuba jari ga cinikayyar.

……………………………………………..

Your Comment

You are replying to: .
captcha